Fitaccen dan wasan da ya lashe kyautar Ballon d'Or Karim Benzema ya amince da yarjejeniyar shekara uku da kungiyar kwallon kafar Al-Ittihad ta kasar Saudiyya kwanaki kadan bayan ya bar Madrid.
Kungiyar ce ta bayyana haka a wani sako mai dauke da hotuna da ta wallafa a shafinta na Twiter ranar Talata.
Dan wasan na Faransa, mai shekara 35, ya yi bajinta sosai a fagen tamaula inda ya ci Kofin Gasar Zakarun Turai sau biyar sa’annan ya ci La Liga sau hudu a shekaru 14 da ya shafe a Real Madrid.
Bayan Cristiano Ronaldo, Benzema ne dan wasan da ya fi cin kwallo a tarihin Real Madrid inda ya jefa kwallaye 354.
A hira ta musamman da aka yi da shi a matsayinsa na sabon dan wasan Al-Ittihad, Benzema ya ce "wannan sabon kalubale ne a gare ni, kuma sabuwar rayuwa. Na zaku na soma atisaye.
Zan yi bakin kokarina wurin lashe gasa, da zura kwallaye da burge 'yan kallo da kuma shugaban kungiyar."
Ya kara da cewa gasar cin kofin kalubale ta Saudiyya tana da kyau kuma tuni fitattun 'yan wasa suka rumngume ta ciki har da Ronaldo.