Ana rade-radin cewa Messi zai tafi Saudiyya domin murza leda. Hoto/Getty

Lionel Messi ya yi watsi da ihun da magoya bayan Paris Saint-Germain [PSG] suka yi masa a yayin da yake buga wasansa na karshe a kungiyar a karawar da Clermont ta doke su da ci 3-2.

Magoya bayan PSG sun rika yi wa shahararren dan kwallon na dunia ihu ranar Asabar a filin wasa na Parc des Princes lokacin da aka kira sunansa a amsa-kuwwa.

Mintuna kadan bayan haka, Messi ya shiga filin wasa yana murmushi, inda yake rike da hannun dansa mai shekara uku wanda ya sumbata kafin a dauki hoto na tawagarsu sannan a soma wasa.

"Ina so na gode wa kungiyar, da birnin Paris da jama'arsa bisa shekara biyu da na yi. Ina yi muku fatan alheri," in ji Messi a hirarsa da aka wallafa a shafin intanet na kungiyar.

A shekaru biyu da ya yi a PSG, Messi ya lashe kofuna biyu na gasar League 1 da Kofin Zakarun Faransa, ya zura kwallaye 32 sannan ya taimaka aka ci kwallaye 35 a dukkan gasar da ya fafata.

Messi ya ci kwallo a Strasbourg makon jiya inda suka tashi 1-1 lamarin da ya taimaka wa PSG lashe kofin na League 1 karo na 11.

Kwallon ita ce kwallo ta 496 da ya ci a tarihinsa, kuma hakan ya bai wa dan wasan na Argentina damar karya tarihin da Cristiano Ronaldo ya kafa na wanda ya fi zura kwallo a manyan gasa biyar na Turai.

Dan wasan bai amince ya tsawaita zamansa a PSG kuma ana rade-radin cewa zai tafi Saudiyya don taka leda inda zai samu karin kudi sosai fiye da Ronaldo.

Kazalika ana hasashe zai tafi Inter Miami sai dai kungiyar ba za ta iya kashe miliyoyin dala da Saudiyya za ta bayar don daukar dan wasan ba.

PSG ce a kan gaba da ci 2-0 bayan dan wasan da zai bar ta Sergio Ramos ya ci kwallo a minti na 16 da kuma fenaretin da Mbappe ya ci a minti na 21.

Sai dai Clermont ta farke kwallayen kafin a tafi hutun rabin lokaci ta hannun Johan Gatien da Mehdi Zeffane. Grejohn Kyei ya zura kwallon da ta ba su nasara a minti na 63.

TRT World