Bayanan suna fitowa ne yayin da jami’ain Saudiyya sun je birnin Paris da Madrid, don kokarin kammala cinikin Messi da Benzema. / Hoto: Reuters Archive

Luka Modric da Hugo Lloris na daga cikin jerin sama da ‘yan wasa 10 da kulob-kulob na kasar Saudiyya ke son siya, inda Lionel Messi da Karim Benzema ke kan gaba, kamar yadda daya daga cikin wadanda ake cinikin da su ya tabbatar.

Sergio Ramos da Jordi Alba da Sergio Busquets da N’Golo Kante da Angel Di Maria da Roberto Firmino na daga cikin shahararrun ‘yan wasan da suka buga Gasar Cin Kofin Duniya da kuma Gasar Zakarun Turai.

Kuma suna daga cikin jerin ‘yan wasan da kulob-kulob na Saudiyya ke nema, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Bayanai na baya-bayan nan na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an na Saudiyya ke Paris da Madrid domin karkare kulla yarjejeniya da Messi da kuma Benzema.

Kamar yadda majiyoyi suka bayyana, hakan zai ba su dama su bi Ronaldo domin ci gaba da taka leda a kasar Larabawa.

Hukumomin Saudiyya “na magana da sama da ‘yan wasa 10, akasarinsu sun ci kofin duniya ko kuma Gasar Zakarun Turai, inda za su shiga Gasar Kwallon Saudiyya a kaka mai zuwa,” in ji majiyar.

Baya ga Messi, “jerin sunayen sun hada da Benzema da Ramos da Di Maria da Modric da Hugo Loris da Kante da Firmino da Alba da Busquets”.

“Bayan an yi musu tayi mai tsoka, za su yi wasa a gasa wadda ake matukar goggaya,” in ji majiyar, inda ta kara da cewa Saudiyya na son “kammala duka yarjejeniyar” kafin a soma sabuwar kaka a 11 ga watan Agusta.

Tattaunawa da manyan ‘yan wasan duniya

A gefe guda, wani jami’in gwamnatin Saudiyya ya ce hukumomi suna gudanar da tattaunawa tare da ‘manyan ‘yan wasan duniya’.

Jami’in ya ce, “Manufar ita ce kafa kakkarfar gasa da za a yi gogayyar irin wadda za ta daukaka darajar kungiyoyin wasanni na Saudiyya”.

Duka ‘yan wasan da aka jero manya ne a duniya, wadanda ke daf da kammala rayuwarsu ta kwallo.

Idan ka cire mai tsaron raga Hugo Lloris, wanda yake da sauran shekara daya a Tottenham, duka sauran a wannan watan za su kare kwantiraginsu.

Kasar Saudiyya, karkashin Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, yana kokarin inganta matsayin kasar mara karsashi, kuma ya janyo hankalin ‘yan yawon bude ido da masu zuba jari, musamman ta amfani da wasanni.

Kasar wadda ta fi kowa fitar da man fetur, ta zuba daruruwan miliyoyi a harkar wasanni, kamar siyo Ronaldo, da gasar tseren mota ta Formula One, da kuma gasar gwaf ta LIV Golf tour.

TRT World