Al Hilal ta Saudiyya ta dauki dan wasan Senegal Kalidou Koulibaly daga Chelsea

Al Hilal ta Saudiyya ta dauki dan wasan Senegal Kalidou Koulibaly daga Chelsea

Rahotanni sun ce kungiyar ta kasar Saudiyya za ta bai wa dan wasan zunzurutun kudin da ya kai $21.61m.
Koulibaly ya zura kwallo biyu a wasanni 32 da ya buga wa Chelsea a dukkan gasa bayan  ta saye shi daga Napoli a watan Yulin da ya gabata. / Hoto: AFP

Dan wasan Senegal Kalidou Koulibaly ya tafi kungiyar kwallon kafar Al Hilal da ke Saudiyya daga Chelsea, kamar yadda kungiyoyin biyu suka bayyana.

"Za mu ci gaba da aiki tare don kafa tarihi," a cewar wani sako da Al Hilal ta wallafa a Twitter ranar Lahadi, wanda yake dauke da bidiyon Koulibaly.

Kungiyar ta ce Koulibaly ya sanya hannu a kwangila zuwa 2026 ko da yake ba ta bayyana adadin kudin da za ta biya shi ba. Amma kafafen watsa labaran Birtaniya sun rawaito cewa Al Hilal za ta bai wa dan wasan kusan fam miliyan 17 ($21.61m).

"Na zo nan don yin kwallo da mutanen da ke da manufa a yanzu da kuma nan gaba," in ji dan wasan da ya lashe gasar Kofin Afirka.

Koulibaly ya zura kwallo biyu a wasanni 32 da ya buga wa Chelsea a dukkan gasa bayan ta saye shi daga Napoli a watan Yulin da ya gabata.

Dan wasan mai shekara 32 shi ne na biyu da ya tafi Al Hilal daga kungiyar da ke buga gasar firimiya bayan dan wasan Portugal Ruben Neves ya tafi can daga Wolverhampton Wanderers ranar Juma'a.

Kungiyoyin Saudiyya na jan hankalin 'yan kwallo

Kungiyoyin da ke buga gasar lig-lig na Saudiyya suna ci gaba da jan hankalin 'yan wasan da ke fafatawa a Turai tun bayan da Cristiano Ronaldo ya tafi Al Nassr a watan Janairu.

Al Ittihad ta sayi dan wasan da ya lashe kyautar Ballon d'Or Karim Benzema a farkon watan nan, yayin da kuma kungiyar ta tabbatar da cewa za ta dauki tsohon dan wasan Chelsea N'Golo Kante.

Al Hilal ita ce kungiyar da ta fi lashe kofuna a Saudiyya da Asia inda ta dauki kofi 66.

Kafafen watsa labaran Sifaniya sun bayyana cewa kungiyar tana dab da daukar dan wasan tsakiyar Manchester City Bernardo Silva.

TRT Afrika da abokan hulda