Za a sake dambacewa tsakanin Oleksandr Usyk da Tyson Fury a ranar Asabar da dare a Saudiyya.
A damben da aka yi da farko, Usyk ne ya yi nasara bayan ra'ayin alƙalai ya zo ɗaya a makin da suka bayar, inda ya zama gwarzon dambe ajin babban nauyi. Tun bayan nan ne Usyk ya rabu da kambun IBF wanda a halin yanzu Daniel Dubois yake riƙe da shi.
A halin yanzu wannan damben da za a yi, kambun WBC da WBA da WBO za su zama a kan layi a wurin damben a Riyadh — wanda a nan ne aka yi damben farkon a watan Mayu.
Usyk ya sha da ƙyar a littafin sakamako na alƙalai biyu, 115-112 da kuma114-113. Sai kuma ɗayan alƙalin ya ba su sakamakon 114-113.
Tun daga zagayen farko har zuwa na bakwai, Fury ne a kan gaba a duka sakamakon alƙalan, sai dai daga baya Usyk ya yi ta tasowa. Usyk ya kusan doke abokin hamayyarsa a zagaye na tara, inda ya yi masa kwab ɗaya kafin ƙaraurawar da aka kaɗa ta ceto Fury.