'Yar wasan gaban Nijeriya Asisat Oshoala ta kulla yarjejeniyar da kulob din Bay FC da ke Amurka, kamar yadda kungiyar ta bayyana ranar Alhamis.
'Yar wasan da ta lashe kyautar gwarzuwar 'yar wasan Afirka sau shida ta koma kulob din na San Jose ne daga kungiyar kwallon kafa ta Sifaniya, Barcelona.
Oshoala, mai shekara 29, ta lashe kofin gasar lig din Sifaniya hudu tare da kofin Zakarun Turai biyu a Barca, inda ta zura kwallaye 107 a raga a wasanni 149 da ta buga.
Kafin ta koma Sifaniya, 'yar wasan ta yi wasa a Ingila inda ta buga wa Liverpool da Arsenal kuma ta yi wasa a China inda ta buga wa Dalian WFC.
Ta yi wa Nijeriya wasa a gasar cin kofin duniya sau uku kuma ta lashe gasar cin kofin Afirka ta mata sau uku a kasarta.
'Rana mai muhimmanci'
"Samun damar karo 'yar wasa mai inganci tare da kwarewa da kuma nasarori kamar Asisat, ta sa wannan rana ta kasance mai cike da farin-ciki da muhimmanci ga kulob din da kuma gasar kwallon kafar mata ta Amurka (NWSL)," in ji babbar manajar Bay FC, Lucy Rushton.
"Ta zo da tunani mai inganci a filin wasa tare da gudu da kuma kwarewa da zai sa ta yi jagoranci inda za ta bai wa 'yan wasan da ke tare da ita damar bayyana kwarewarsu. Asisat mai zura kwallo raga ce wadda aka tabbatar da kwarewarta a duniya kuma ta zo nan ta ci gaba da yin hakan tare da Bay FC."
An kafa kulob din da ke California ne a watan Afrilun bara kuma zai yi amfani da filin wasa daya tare da kulob din San Jose Earthquakes da ke buga gasar lig ta maza ta Amurka .