Kulob 20 ne za su halarci gasar Firimiya ta Nijeriya ta bana./Hoto: Others

Umar Yunus, daga Jos

Gasar ƙwallon ƙafa ta Firimiya ta Nijeriya, wato Nigerian Premier League, ita ce babbar gasar ƙwallon ƙafa da ake gudanarwa a kowace kakar ƙwallon ƙafa a ƙasar tun 1972.

Alƙaluma na baya bayan nan, na Hukumar Tarihi da Ƙididdiga ta Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya, wato International Federation of Football History and Statistics, IFFHS a taƙaice, sun nuna cewa, gasar Firimiya ta Nijeriya, ita ce ta Tara a Afrika, kuma ta 77 a cikin gasannin 80 na ƙasashen duniya.

Yayin da ake soma gasar ta kakar 2023/2024 a yau Asabar 30 ga watan Satumba, kulob-kulob da za su halarci gasar sun shirya tsaf da zimmar farawa da ƙafar dama.

An gudanar da kakar da ta gabata cikin tsarin rukuni, inda aka raba kulob 20 zuwa rukunin A da B, kowane rukuni ya ƙunshi kulob 10.

Daga bisani an zaɓi kulob uku mafi ƙwazo daga kowane rukuni, suka kara tsakaninsu a gasar Super Six, a birnin Lagos, inda Enyimba suka zama zakarun gasar ta 2022/2023, bayan sun samu maki mafi yawa a ƙarshen gasar.

Wannan nasara ita ce karo na 9 da Enyimba ta lashe gasar ta Firimiya, adadi mafi yawa a tarihin gasar.

Tsarin gasar a kakar 2023/2024 ya sha bamban da na 2022/2023 kamar yadda kwamitin wucin gadi na hukumar gudanar da gasar ya bayyana.

A cewarsa, kulob 20 ne za su halarci gasar kai-tsaye. Waɗannan kulob ɗin sun haɗa da ragowar 16 na kakar da ta gabata da kuma sababbi guda 4 da suka hauro daga Nigerian National League NNL ( gasar ƙwallon ƙafa ta biyu mafi girma bayan ta firimiya).

Waɗannan kulob ɗin za su buga da junansu, wato kowa zai kara da kowa, a gida da waje, har zuwa ƙarshen kakar, lokacin da za a ayyana kulob ɗin da ya samu maki mafi yawa a matsayin zakara.

Ƙalilan ne daga cikin kulob ɗin da ke halartar gasar firimiya ta Nijeriya ƴan kasuwa suka mallaka, domin mafi yawansu mallakin gwamnatocin jihohi ne, kuma su suke ɗaukar nauyin gudanar da su.

Ƙalilan ne daga cikin kulob ɗin da ke halartar gasar firimiya ta Nijeriya ƴan kasuwa suka mallaka, domin mafi yawansu mallakin gwamnatocin jihohi ne, kuma su suke ɗaukar nauyin gudanar da su./Hoto: Others

Wannan bai rasa nasaba da ƙarancin ƴan kasuwa a harkar ƙwallon ƙafa a Nijeriya.

Sporting Lagos na ɗaya daga cikin kulob hudu da suka hauro firimiya a bana, kuma ya kafa tarihi kasancewa shi ne kulob na farko a tarihin gasar da ya samu nasarar kai wa wannan matsayin a shekara farko da kafa shi.

Tun lokacin da hukumar kula da gasar firimiya ta ayyana buɗe kasuwar saye da sayar da ƴanwasa, kulub suka duƙufa wajen ɗauko sabbin ƴanwasa daga wasu kulub ɗin da kuma sayarwa ko kuma ƙyale ƴanwasa da kwantiraginsu ya ƙare su tafi wasu kulub ɗin.

Wasu ƴan wasan ma daga ƙetare ake ɗauko su, musamman ƙasashen Afrika. Baya ga haka, kulob suna tsananta bai wa ƴan wasansu horo na musamman da kuma gwada dabarun yin nasara a kan abokan karawa.

Bugu da ƙari, kulob suna buga wasannin sada zumunci tsakanin su da wasu kulob manya da kanana.

Wani lokaci, sukan halarci ƙwarya ƙwaryar gasa, da zimmar ganin tasirin atisayen da suka gudanar da kuma tantance ƙwazo da ƙoshin lafiyar ƴanwasansu.

Najib Isma'ila Mabo, mai horar da ƴan wasan ne a Nijeriya, kuma ya ce matakan da kulob ke ɗauka na kimtsawa sosai gabanin fara kowacce kakar ƙwallon ƙafa yana da matuƙar tasiri wajen ɗorewar ƙungiya a gasar.

"Babban maƙasudin shirye-shirye da kulob ke yi gabanin fara kakar ƙwallon ƙafa, shi ne su gwada ƙwarewar ƴan wasansu kafin kakar ta kankama, saboda idan ba a gwada ƙwarewar ƴan wasa ba, za a sha kunya. Wataƙila wasu kulob ɗin sun sha da kyar, ko kuma ba su gamsu da ƙwazonsu a kakar da ta gabata ba, ka ga ko ai dole su sake lale," ya jaddada.

Najib Mabo ya ce  hanyoyi uku ne manyan kulob ke amfani da su wajen ɗauko ƴan wasa./Hoto:Others

A cewarsa, hanyoyi uku ne manyan kulob ke amfani da su wajen ɗauko ƴan wasa: ta gayyata ko yaye masu tasowa a ƙaramar ƙungiyarsu (feeder team)ko ta saye kai-tsaye daga wani kulob. "

Kulob kan gayyaci wasu zaɓaɓɓun ƴan wasa daga waje da suke ganin sun kawo ƙarfi, su zo su gwada sa'arsu, ko su ɗauko daga ƙaramar ƙungiyarsu (feeder team) ko kuma su zuba zunzurutun kuɗi su sayo duk ƴan wasan da suke da muradi daga wasu kulub ɗin a gida Nijeriya har ma da ƙasashen ƙetare.

Maganar gaskiya ita ce, batun gasar Firimiya batu ne na ƙwararrun ƴan wasa. Saboda haka, duk kulob ɗin da ke son kai wa gaci, wajibi ne ƴa ɗauko 'yan wasa bisa cancanta," in ji Mabo.

To ko waɗanne kulob ne ake hasashen za su lashe gasara a wannan karon? Jibril Muhammad wani mai sharhi ne a kan wasannin kuma ya ce kulob ɗin da suka nuna da gaske suke ba su fi guda uku ba.

"A ganina, Rivers United ne za su iya lashe gasar ta bana saboda ba su rabu da galibin ƴan wasansu ba; hasali ma, ƙarin wasu gogaggu suka sayo. Sannan kuma, a halin yanzu, suna buga Gasar Zakarun Afrika; abin da ke nuna jikin ƴan wasansu ya daɗe da ɗaukar ɗumi. Wannan babban fifiko suke da shi a kan waɗanda yanzu suka fara shiri."

Jibril ya ci gaba da cewa, sauran kulob ɗin da yake hasashen za su iya lashe gasar ta bana, sune Enyimba da Remo Stars, duba da irin ƙoƙarin da suka yi a bara, sannan sun ɗauko ƙarin fitattun ƴanwasa da suke ganin za su iya cire musu kitse a wuta.

A cewarsa, "Ƴan wasan waɗannan kulob ɗin sun jima tare, sun fahimci salon taka ledar junansu, saɓanin kulob ɗin da yanzu suke ƙoƙarin haɗa ƴan wasa."

Batun alƙalancin wasa yana taka muhimmiyar rawa wajen ƙara wa wasanni armashi.

Sai dai a lokuta da dama, ana zargin alƙalan wasa da yin maguɗi. Najib Mabo ya tabbatar da cewa hakan na faruwa, amma sakamakon mataki da hukumar gasar firimiya ta fara ɗauka a bayabayan nan, ana samun sauƙin lamarin.

"Idan an lura, yanzu kulub na iya fita waje ya yi nasara saɓanin yadda lamarin yake a da, inda dole kulub ya ci wasansa a gida ko da tsiya ko da tsiya tsiya. Yanzu ana dakatar da duk alƙalin wasa da aka samu hanunsa a almundahana," a cewar Najib Mabo.

Magoya bayan kulub suna bayar da gudummawa wajen kawo tarnaƙi lokacin wasa, ta hanyar tursasawa, ko matsa lamba ko tsoratarwa ko kuma ma a wani lokaci cutar da alƙalin wasa da sauran jami'an wasa, idan suka ƙi daka ta tasu, abin da Jibril Muhammad ya ce yana kawo nakasu ga harkar ƙwallon ƙafa a Nijeriya.

Ya ci gaba da cewa rashin zaƙulowa da hukunta magoya bayan kulob masu tayar da rikici lokacin wasa shi ya sa ɗabi'ar take ci gaba da yaɗuwa.

Ya shawarci kulub da su dinga ɗaukar matakin kora ko dakatar da duk wani magoyin bayansu da suka samu da laifin kawo hayaniya a wasa, tunda abin kan ƙare a kansu ne; inda a kan ci tararsu, ko tilasta musu buga wani adadin wasanni ba tare da magoya bayansu ba, ko kuma ma, a ɗauke su kwata kwata daga garinsu, a kai su can wani gari, su dinga buga wasanninsu.

Bisa ga dukkan alamu, kakar ta bana, za ta yi armashi, idan aka yi la'akari da matakan da masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa ke ɗauka, da kuma tabbacin da mashirya gasar ke bayarwa na inganta ta.

TRT Afrika