Washington Wizards kungiyar NBA dake kan gaba ta samar da shafin sadarwa da Larabci

Washington Wizards kungiyar NBA dake kan gaba ta samar da shafin sadarwa da Larabci

Kungiyar na fatan shafukan sadarwa na zamani na yanar gizo za su taimaka mata wajen samun karbuwa sosai a Gabas ta Tsakiya.
wizards

A kokarin su na kara yaduwarsu a fagen kasa da kasa, kungiyar kwallon kwando ta Washington Wizards ta zama kungiya ta farko ta NBA da ta kaddamar da shafin sadarwa na Larabci.

Za a iya samun shafin @WizardsArabic a shafukan Twitter da Instagram, kuma takensu shi ne #yallaWizards.

Shafukan sadarwa na nazamani na Larabci na Wizards za su bayar cikakken bayani game da kungiyar a kakar wasanni gaba daya, wanda zai hada da nazarin wasanni, wanzuwar kafafan yada labarai, labarai, abubuwan da suke afkuwa a boye da kuma ra’ayoyin magoya baya.

Kungiyar na fatan wadannan shafuka za su taimaka mata sosai wajen samun karin magoya baya a Gabas ta Tsakiya. Tana kuma shirin samar da shafiin yanar gizo a harshen Larabci a nan gaba.

Shugaban wasanni da jin dadi na kungiyar Jim Van Stone ya shida cewa “Mun ji dadin kara harshen Larabci a jerin yarukan shafukanmu na sada zumunta na yanar gizo.” Ya kara da cewa “Mun san masu magana da Larabci dake goyon bayan kwallon kwando za su ji dadin bayanan da za mu dinga fitarwa kuma za zama makusantan Wizards.”

Sanarwar da kungiyar ta fitar a hukumance ta ce, sabbin shafukan za su samar da sabbin dandali ga Amurkawa-Larabawa da Larabawa zalla da suke kallon wasannin NBA a lardunan Columbia, Maryland da Virginia.

Wizards sun kuma taimaka wajen girmamar wasannin ta hanyar karbar bakuncin kananan asibitocin matasa na wasanni, wasannin yanar gizo da kuma aiyukan farantawa al’uma a Gabas ta Tsakiya.

Kungiyar Wizards na da hadin kai da kamfanin jiragen sama na Etihad, wanda shi kadai ne ke hada gwiwa a matakin kasa da kasa da ‘Washington Capital’, ‘Washington Mystics’ da ‘Capital One Arena’ tun 2015.

A ‘yan shekarun nan, kungiyar Wizards ta samar da shafukan sadarwa na yanar gizo domin magoya bayanta dake kasashen China, Japan da Isra’ila. Sannan tana da tasha a yaren Spaniyanci @vamoswizards wadda aka kaddamar a watan da ya gabata.

NBA na haren yankin Gulf

A watan November da ya gabata, an sanar da kulla wata yarjejeniya ta shekaru da dama tsakanin NBA da Sashen Raya Al’adu na Abu Dhabi.

A makon da ya gabata, an buga wasannin share fage tsakanin Milwaukee Bucks da Atlanta Hawks a Etihad Arena dake Tsibirin Yas na Abu Dhabi, wanda shi ne wasan gasar da aka fara bugawa a Hadaddiyar Daular Larabawa da ynkin Gulf.

Mataimakin Kwamishina na NBA Mark Tatum kafin buga wasannin ya bayyana cewa, “Bayan mun buga wasannin a can, zai zama kamar mun buga wasanni a dukkan yankunan duniya. Ya kara da cewa ”Babbar manufarmu da dabararmu ita ce mu tabbatar mtane suna jin su wani bangare ne na wasannin, saboda hakan na da tasiri kan samun magoya baya.

Tsawon lokaci NBA na a wannan yankin, yana yada wasanni tsawon shekaru 35 kuma ya shida manyan zakru daga Kobe Bryant zuwa Hakeem Olajuwon da suka ziyarci Hadaddiyar Daular Larabawa don ganawa da magoya baya.

TRT World