Vinícius ya ji takaicin rashin nasara samun kyautar Ballon d’Or a watan Oktoba, wacce ɗan wasan tsakiya na Manchester City Rodri ya lashe. / Hoto: Real Madrid/X

Daga ƙarshe dai ɗan wasan Real Madrid Vinícius Júnior ya samu nasarar lashe kyautar babban ɗan wasan duniya a ranar Talata.

An zabi Vinícius a matsayin gwarzon ɗan wasa na na shekara inda ya samu lambar yabo ta FIFA ta "gwarzon bana", yayin da 'yar wasan Barcelona Aitana Bonmati ta ci gaba da riƙe kambun kyautar ta kwallon kafa a ɓangaren mata.

Vinícius ya ji takaicin rashin nasara samun kyautar Ballon d’Or a watan Oktoba, wacce ɗan wasan tsakiya na Manchester City Rodri ya lashe, abin da ya sa Vinícius da ƙungiyarsa Madrid suka yi watsi da bikin da aka yi a birnin Paris, don nuna rashin amincewarsu.

Ɗan wasan na gaba na Brazil ya halarci bikin karɓar lambar yabo ta FIFA bayan da ya tafi Doha ranar Litinin tare da Madrid don buga wasan ƙarshe na cin kofin Intercontinental da Pachuca.

Tauraruwar Bonmati tana haskakawa

Bonmati ta lashe kyautar Ballon d'Or tsawon shekaru biyu a jere, kuma ta lashe gasar La Liga da kofin Sifaniya da kuma gasar Zakarun Turai a Barcelona a shekarar 2024.

TRT Afrika