Nigeria Super Falcons

‘Yan Nijeriya na tofa albarkacin bakunansu bayan fitar da sabuwar rigar kwallon ‘yan wasa mata na kasar Super Falcons.

Kungiyar ta fitar da hotunan sabbin rigunan a shafukan sada zumunta sanye a jikin Kyaftin din Super Falcons Azeezat Osuola da ‘yar wasan gaba Rasheedat Ajibade.

Rigunan iri biyu ne da launin kore mai haske don wasannin cikin gida da kuma mai adon baki don wasannin waje.

Kamfanin samar da tufafin wasanni na Nike ya fitar da rigunan a ranar Litinin a lokacin da Super Falcons suke shirin halartar Gasar Kasa da Kasa ta mata ta FIFA.

Magoya baya na tofa albarkacin bakunansu ta salo daban-daban.

Wani Mr. Gabriel Owolabi ya ce "Launukan sabbin rigunan sun yi kyau. Launukan sun yi matukar tsuma ni, musamman da yake ba mu faye amfani da jan launi ba wanda shi ne na safar.

"Ina muku fatan alheriLovely colors for our new jerseys. Fascinated by the away colors, using red socks as part of our colors is rare #SuperFalcons a wannan gasa mai zuwa ta #FIFAWomenWorldCup!!!

Shi ma wani STIKS@Stiks1993 ya ce "Kai, gaskiya sun yi kyau matuka.

Kungiyar ta Nijeriya da za ta halarci gasar a karo na 10, a rukunin B tare da masu karbar gasar a bana wato kasashen Ostireliya da Kanada da Tarayyar Ireland.

A watan Yulin bana za a fara gasar.

TRT Afrika