An tashi wasan na sada zumunta Nijeriya na da kwallaye uku, New Zealand kuma na nema / Hoto AA

Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Nijeriya Super Falcons ta doke takwararta ta kasar New Zealand. da ci 3 da 0 a wasan sada zumunci da suka buga.

An buga wasan ne a filin wasanni na garin Antalya da ke kasar Turkiyya.

A minti na 34 da fara wasa ‘yar kwallon kafar Nijeriya Onome Ebi ta ci kwallon farko bayan taimakon da ta samu daga Toni Payne.

Haka aka ci gaba da buga wasan, Nijeriya na da kwallo 1 yayin da New Zealand na nema.

A minti na 49 bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Nijeriya ta sake jefa kwallo daya ta kafar Onyi Echegini.

Désiré Oparanozie ta ciyo wa Nijeriya kwallo ta uku a minti na 94.

An tashi wasan na sada zumunta Nijeriya na da kwallaye uku, New Zealand kuma na nema.

TRT Afrika