Messi ya zura wa kungiyar kwallo 31 sannan ya taimaka aka ci kwallo 34 a wasa 71 da ya fafata a PSG. Hoto/PSG

Paris St-Germain ta dakatar da Lionel Messi tsawon makonni biyu saboda ya kai ziyara Saudiyya a wannan makon ba tare da izinin kungiyar ba.

Kungiyar ta dakatar da Messi ne bayan ta sha kashi a hannun Lorient a wasan da suka buga ranar Lahadi wanda dan wasan ya fafata a cikinsa.

Hakan na nufin fitaccen dan kwallon ba zai buga wasan da za su yi da Troyes da Ajaccio ba a yayin da PSG ke kan gaba da maki biyar a gasar Ligue 1 wadda ake sa ran za ta sake cinyewa a karo na 11.

Watakila ba zai sake buga wa PSG ba, ko da yake hakan ya dangantaka da abin da zai iya faruwa nan da mako biyu.

Messi ya zura wa kungiyar kwallo 31 sannan ya taimaka aka ci kwallo 34 a wasa 71 da ya fafata a PSG, haka kuma ya lashe Kofin Ligue 1 a kakar da ta wuce.

Bayanai sun nuna cewa dan wasan mai shekara 35 ya nemi izinin tafiya Saudiyya don gudanar da harkokin kasuwanci amma aka hana shi.

Kwangilar da Messi ya kulla da PSG za ta kare a karshen kakar wasan da muke ciki, abin da ke nufin wasa uku kawai suka rage masa ya buga a kungiyar.

A bayyane take cewa Messi yana da alaka da Saudiyya, domin ko a watan jiya ya wallafa wani sakon Instagram daga can. Kazalika yana tallata harkokin yawon bude ido na kasar.

A watan Maris, mataimakin shugaban Barcelona Rafael Yuste ya yi ikirarin cewa suna tuntubar Messi da zummar komawa Nou Camp.

TRT Afrika da abokan hulda