Wata kungiyar kwallon kafa ta kasar Turkiyya ta dauki tsohon dan wasan Faransa Nicolas Anelka aiki a matsayin kocinta a ranar Alhamis.
“Maraba, Farfesa! Kulob ɗinmu ya amince da Nicolas Anelka a matsayin shugaba, kamar yadda kungiyar kwallon kafa ta Umraniyespor da ke Istanbul wadda a halin yanzu take rukuni na biyu na Turkiyya, ta wallafa a shafinta na X.
Umraniyespor ta sauka kasan teburi Gasar Super Lig a kakar wasan bara.
Anelka, mai shekara 44, ya kasance tsohon dan wasan Faransa kuma ya buga wasa a manyan fitattatun kungiyoyin kwallon kafa na Turai kamar Paris Saint-Germain da Arsenal da Real Madrid da Liverpool da Manchester City da Chelsea da kuma Juventus.
Tauraron na daya daga cikin manyan 'yan wasan kwallon kafa a zamaninsa sannan gwarzo ne da ya taka muhimmiyar rawa a tsakanin 'yan wasa a Gasar Premier ta Ingila.
Anelka ya shafe kaka daya da rabi a kungiyar Fenerbahce da ya zama zakaran Turkiyya a shekara ta 2005.
A shekarar 2016 ne ya yi ritaya daga buga kwallon kafa bayan ya buga wasa a birnin Mumbai na kasar Indiya.
Anelka ya kasance ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a Gasar Premier da ƙwallaye 19 a kakar wasa ta shekarar 2008 zuwa 2009 a matsayin dan wasan Chelsea.
Ya lashe gasar Zakarun Turai lokacin yana Real Madrid a shekara ta 2000, kafin ya taimaka wa Faransa ta lashe kofin EURO ta 2000.
Anelka ya kasance zakaran gasar Ingila sau biyu, a kungiyar Arsenal a shekarar 1998 da Chelsea a shekarar 2010.
Daga karshe ya jagoranci wata karamar kungiyar kwallon kafa ta Faransa Hyeres a shekarar 2021 bayan horar da kungiyar matasa ta Lille.