Lionel Messi  ya jajanta tare da bayar da kwarin gwiwa ga mutanen Maroko/ Photo: Reuters

Fitaccen dan kwallon kafa na Argentina Lionel Messi, a ranar Lahadi ya jajanta wa Maroko bisa mummunar girgizar kasa da ta yi sanadin mutuwar daruruwan mutane a kasar da ke arewacin Afirka.

"Ina mika ta'aziyya ga dukkan iyalan wadanda iftila'in girgizar kasa ya shafa a Maroko," a cewar zakaran kwallon kafa na duniya Messi a sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

"Ina kara wa dukkan mutanen da suka jikkata da kuma sauran wadanda iftila'in ya shafa karfin gwiwa," in ji shi.

Akalla mutum 2,122 ne suka mutu yayin da 2,421 suka jikkata sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 7 da ta afku a Maroko ranar Juma'a da dare, a cewar ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar.

Iftila'in girgizar kasar ya kasance mafi girma da muni da ya taba afkuwa a kasar cikin shekaru 100, a cewar Cibiyar Nazarin Yanayin Kasa ta Maroko.

TRT Afrika