Fitaccen dan wasan Argentina Lionel Messi ya sanya hannu kan kwangilar shekara biyu a kungiyar Inter Miami da ke fafatawa a Babbar Gasar Lig.
Zai zauna a kungiyar zuwa shekarar 2025.
"Ina matukar jin dadin bude wani sabon babi a sana'ata inda zan kasance a Inter Miami da Amurka," in ji Messi, a wani sako da ya fitar ranar Asabar.
Dan wasan ya bar Paris Saint-Germain bayan kwangilarsa ta kare sannan aka yi ta kai-ruwa-rana tsakaninsa da kungiyar ta Faransa.
A ranar Lahadin nan kungiyar ta Inter Miami za ta gabatar da Messi a gaban 'yan kallo kuma ana sa rai zai soma murza leda ranar Juma'a.
Ana sa rai dan wasan, wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or sau bakwai, zai sa mutane da dama a Amurka su soma sha'awar gasar kwallon kafa ta MLS da kuma ta kasar baki daya, sannan ya sa tawagar Miami ta samu tagomashi.
"Wannan muhimmiyar dama ce kuma tare za mu ci gaba da gina wannan kungiya mai kyau," a cewar Messi.
"Manufar ita ce mu yi aiki tare don cimma burinka da muka sanya a gaba kuma na zaku na soma taimakawa a wannan sabon gina nawa."
Burin Beckham ya cika
Ranar Juma'a ake sa rai Messi zai soma wasa a karawar da Inter Miami za ta karbi bakuncin Cruz Azul a gasar cin kofin Lig, wasan da ake yi tsakanin MLS da tawagogin gasar lig-lig ta Mexico.
Wannan shi ne tagomashi mafi girma da gasar Lig ta Arewacin Amurka ta samu tun bayan da David Beckham, wanda ke cikin mamallakan Inter Miami, ya koma Los Angeles Galaxy a 2007. Ya kaddamar da tawagar MLS a 2020 bayan ya shafe shekaru yana neman inda zai gina filin wasa.
"Shekara goma da suka wuce lokacin da na soma tunanin hada sabuwar tawaga a Miami, na ce babban burina shi ne na dauko manyan 'yan wasa a duniya don kawo su wannan birni mai ban sha'awa.
Burina shi ne na kawo 'yan wasan da ke da irin ra'ayina lokacin da na zo LA Galaxy domin na taimaka wajen bunkasa kwallon kafar Amurka," in ji Beckham a wata sanarwa da ya fitar.
"Yau burina ya cika."