Kungiyar kwallon kafar Inter Miami da Lionel Messi sun lashe Kofin Leagues Cup ranar Asabar bayan sun doke Nashville da ci 10-9 a bugun fenareti.
Kungiyoyin sun yi bugun fenareti ne bayan wasan ya tashi da ci 1-1.
Messi ne ya zura kwallon farko a minti na 24 da soma wasa amma Fafa Picault ya farke wa Nashville bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
Bayan Leonardo Campana ya kasa yin amfani da damarsu ta karshe, an tafi bugun fenareti wanda ya kai ga har gololi biyu sun buga fenareti - amma golan Inter Miami Drake Callender ya kade kwallon da takwaransa na Nashville Elliot Panicco ya cilla masa.
Lionel Messi ya ci kwallaye goma a gasar Leagues Cup da ya buga wa Inter Miami.
Tsohon dan wasan Barcelona, wanda ya lashe kyautar ballon d'or sau bakwai, ya zura kwallo a duka wasanni bakwai da ya buga wa Miami tun da ya soma murza leda a kungiyar.