Kwaca-kwacai da 'yan jarida a Turai ne suka kada kuri'u da aka yi amfani da su wajen fitar da sunayen wandanda za fitar da masu kyaututtukan UEFA din a cikinsu:Hoto/Reuters

Dan wasan Argentina, Lionel Messi na cikin ‘yan wasa uku da aka fitar da sunayensu don zaben dan wasan da ya fi iya murza leda a Turai a kakar wasan da ta gabata.

Kyaftin din da ya taimaka wa kasarsa cin gasar kofin duniya, wanda ya bar Turai zuwa Inter Miami yana takara ne da ‘yan wasan Manchester City, Kevin de Bruyne da kuma Erling Haaland.

Messi ya lashe samun kyautar ta UEFA sau biyu cikin shekara 12 da aka yi ana bayar da kyautar.

A shekarun da tsohon kulob dinsa Barcelona ta lashe kofin gasar zakarun Turai ne Messi ya samu kyautar.

Ita kuwa machester City ce ta lashe kofin Zakarun Turai a kakar da ta gabata.

Kocin Machester City, Pep Guardiola, shi ake ganin ya fi cancanci samun kyautar kocin da ya fi basira a Turai a jerin maza duk da cewa Simeone Inzaghi na Inter Milan da kuma Luciano Spalleti na Napoli na cikin kwaca-kwacan da aka tsayar domin kyautar.

Za a bayyana wadanda suka ci kyaututtukan ranar 31 ga watan Agusta a birnin Monaco a lokacin da za a fitar da jadawalin gasar Zakarun Turai.

A mako mai zuwa ne dai za a fitar da wadanda za su iya samun kyatuttuka a cikin mata bayan an kammala gasar cin kofin duniya ta mata, in ji hukumar UEFA.

Kylian Mbappé, wanda ya buga wasa da Messi a Paris Saint-Germain, shi ya zo na shida a cikin ‘yan wasan da suka samu kuri’un ‘yan jarida da kwaca-kwacen Turai duk da cewa shi ya fi zura kwallo a raga a gasar cin kofin duniya da ga aka yi a bara.

‘Yan wasan tsakiyar Man City, Ilkay Gündoğan da Rodri sun fi Mbappé samun kuri’u.

Dan wasan Inter Milan daya tilo da ya samu kuri’u shi ne Marcelo Brozović, yayin da Cristiano Ronaldo da Neymar da suka koma Saudiyya ba su samu kuri’a ko daya ba.

TRT Afrika