Hukumar Kwallon Kafa ta Turkiyya ta mika bukatar karbar bakuncin gasar kwallon kafar Turai, EURO, a 2028 ko 2032, kamar yadda UEFA ta sanar ranar Laraba.
"Hukumar Kwallon Kafa ta Turkiyya ta bukaci karbar bakuncin EURO 2028 ko 2032," a cewar sanarwar ta UEFA.
Su ma Birtaniya da Ireland - wadanda ke wakiltar hukumomin kwallon kafar Ingila, Arewacin Ireland, Jamhuriyar Ireland, Scotland, da Wales - sun mika bukatarsu ta hadin gwiwar karbar bakuncin gasar ta EURO 2028.
Hukumomin UEFA sun ce za su yi nazari kan kowacce bukata nan da watanni masu zuwa, sannan a watan Oktoba manyan jami'anta za su kada kuri'a kan kasar da ta dace ta karbi bakuncin gasar a 2028 da 2032.
AA