Shugaban hukumar ba da kyaututtukan bajinta a wasan ƙwallon ƙafa na duniya ta Ballon d’Or, Vincent Garcia, ya ce akwai waɗanda suka lashe kyautar a baya da ke ƙauracewa kaɗa ƙuri'ar zaɓen wanda zai lashe wasu rukunin kyaututtukan, duk da an ba su dama.
Garcia ya ba da misali da gwarzon ɗan wasa Cristiano Ronaldo, wanda ya lashe babbar kyautar a rukunin maza har sau biyar, wanda kuma hakan ya ba shi damar kaɗa ƙuri'a don zaɓen wanda ya cancanci kyautar a rukunin matasa.
Sai dai Garcia ya nuna cewa, Ronaldo 'yana fushin' cewa ba ya cikin jerin waɗanda suka cancanci lashe gwarzon ɗan ƙwallo a bana, kuma hakan ya sa ya ƙi saka ƙuri'a kuma ya ƙauracewa halartar bikin.
Da ma dai a bana ne aka taɓa ganin babu sunayen Ronaldo wanda ke buga wasa a Saudiyya, da kuma babban abokin hamayyarsa, Lionel Messi da ke taka leda a Amurka, a jerin gwarazan na da za su iya lashe kyautar ta 2024.
Ronaldo ɗan asalin Portugal da ke buga wa Al Nassr a yanzu, ya lashe kyautar Ballon d'Or karo biyar, yayin da Messi ɗan asalin Argentina da ke buga wa Inter Miami, ya lashe kyautar har karo takwas.
Ƙin halartar biki
Shugaban na Ballon d'Or, Vincent Garcia wanda kuma shi ne editan mujallar France Football, wanda ke ba da kyaututtukan bajinta a ƙwallo tun 1956, ya ce ba shi da tabbacin ko Ronaldo zai halarci bikin na bana.
Garcia ya faɗa wa jaridar The Times cewa, "Zakarun kyautar suna da damar su halarci duk wani bikin ba da kyautar, amma ba dukkansu ke zuwa ba, wasu suna jin haushin mu."
Ya ƙara da cewa, "Ba ni da tabbas Cristiano yana cikinsu, ba na magana da shi kai-tsaye, amma na san cewa tsaffin zakarun gasar suna iya kaɗa ƙuri'a a kyautar Kopa Trophy, ta matasan 'yan wasa, kuma Cristiano bai yi zaɓen ba a bara da bana."
A yau Litinin ne za a bayar da kyaututtukan Ballon d’Or na 2024 a wani ƙayataccen biki a birnin Paris na Faransa.
Baya ga Jude Bellingham da Rodri 'yan Ingila, ana fifita saka ran cewa ɗan wasan Brazil da Real Madrid, Vinicius Jr ne zai lashe kyautar a cewar shafin Goal.com.