CAF ta kafa kwamitin ladabtarwa domin bincike kan abin da ya faru tsakanin ɓangarorin biyu. / Hoto: Getty Images

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka CAF ta bayar da maki uku ga Nijeriya (3-0) da kuma cin tarar Libya dala 50,000 sakamakon rashin buga wasa da Libiya.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban na CAF, Patrice Motsepe ya bayyana cewa ana gudanar da bincike mai zurfi dangane da rashin jituwar da aka samu a yayain wasan fitar da gwanin da ya kamata a buga tsakanin Nijeriya da Libiya a ƙasar ta Libiya.

Motsepe ya jaddada cewa hukumar ta CAF ba za ta lamunci duk wani rashin ƙwarewa ba ko kuma rashin adalci a wasan ƙwallon ƙafa a Afirka ba.

A wata sanarwa da shugaban kwamitin ladabtarwa na hukumar Ousmane Kane ya fitar a ranar Asabar, an ɗauki matakin bai wa Nijeriya wannan makin ne bayan kwamitin ladabtarwar da aka kafa ya yi bincike kan abin da ya faru tsakanin Nijeriya da Libiya.

Rashin jituwa tsakanin Nijeriya da Libya

Tun da farko ‘yan wasan na Super Eagles da ma'aikata sun tashi zuwa Libya ranar Lahadi 13 ga Oktoba da daddare, sai dai an karkatar da jirginsu zuwa filin jirgin sama na Al Abraq na Ƙasa-da-Ƙasa, maimakon na Benghazi inda da farko nan aka tsara za su sauka, wanda ya zarce nisan kilomita 200, kuma sai an yi tafiyar awa uku da rabi kafin a je otal ɗinsu.

Ɗaya daga jami'an Filin Jirgin Saman na Al Abraq na Ƙasa-da-Ƙasa ya shaida wa manema labarai cewa tawagar ta Nijeriya ta ƙi buga wasan ne a Libya don ƙaurace wa wasan neman shiga gasar AFCON da Libya a ranar Talata.

Jami'in ya ce 'yan wasan na Nijeriya sun yanke hukuncin komawa gida ne maimakon buga wasan. Wasu daga 'yan wasan sun yi zargin cewa an bar su ba tare da abinci da ruwa ba.

Sai dai bayan faruwar wannan lamarin, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ta ƙaddamar da bincike kan abin da ya sa tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ta ƙi buga wasan neman shiga gasar AFCON da Libya inda suka ambaci "wulaƙancin" da aka yi musu a filin jirgin sama na Libya.

TRT Afrika