Rodri haifaffen birnin Madrid ne kuma shekarunsa 28 a halin yanzu. / Hoto: (AFP)

Bayan da ɗan wasan Manchester City, Rodri ya doke ɗan wasan Real Madrid Vinicius Jr wajen lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa na duniya ta Ballon d'Or, a yanzu tauraruwar Rodri tana ƙara haskakawa a duniyar wasa.

Hasali ma, rahotanni na cewa Real Madrid tana shirin sayar da ɗan wasanta Aurelien Tchouameni, don samar da gurbin kawo Rodri ƙungiyar, domin ci gaba da riƙe kambinta na kulob ɗin da ya fi kowanne ƙima a duniya.

A kakar bana, Madrid tana fama da rashin kumari daga 'yan wasant na tsakiya, tun bayan tafiyar Toni Kroos wanda ya yi ritaya. Ana kallon wannan matsalar ta janyo musu rashin nasarar a hannun Barcelona a makon jiya inda aka ragargaje su da ci 4-0.

A yanzu dai, shugaban ƙungiyar Florentino Perez, da kocinsu Carlo Ancelotti sun bazama neman hanyoyin warware wannan matsala, inda rahotanni ke cewa ba su gamsu da ƙoƙarin Tchouameni da Eduardo Camavinga a tsakiyar filin wasa ba.

Rodri zai amsa?

Duk da raɗe-raɗin cewa Madrin na son tura tayin sayo Rodri, wanda ɗan asalin Sifaniya ne, ba dole gwarzon ɗan wasan ya yi hanzarin amsa tayin baro Man City ba, sakamakon wasu dalilai da shafin Goal ya hasaso.

Da farko dai, Rodri yana da tarihin taka leda a Atletico Madrid, wadda babbar abokiyar hamayyar Real Madrid ce kasancewar suna gari guda. Rodri ya buga kakar wasa ɗaya a Atletico, kuma ya samu farin jini wajen masoya kulob ɗin.

Dalili na biyu shi ne martanin da Real Madrid ta yi bayan da Rodri ya doke Vinicius a lashe Ballon d'Or, inda aka ga tarin 'yan wasa da tsaffin 'yan wasan Madrid suna nuna rashin darajawa ga ɗan wasan.

A yanzu dai za a saurari buɗe kasuwar cinikin 'yan wasa ta watan Janairun mai zuwa don ganin yadda za ta kaya a Madrid, kan neman mafita da suke game da matsalar tawagarsu a tsakiyar fili.

TRT Afrika