Bikin bayar da kyautar Ballon d'Or ta bana ya bar baya da ƙura, bayan da ɗan wasan Manchester City ɗan asalin Sifaniya, Rodri ya doke ɗan wasan Real Madrid ɗan asalin Brazil, Vinicius Junior.
A yanzu dai rahotanni na cewa Vinicius ya yi amanna da cewa rashin nasararsa tana da alaƙa da fafutukarsa kan kawar da wariyar launin fata daga harkar wasanni.
An bar Real Madrid da Vinicius da ma masoyansu cike da al'ajabi a daren Litinin, bayan da ta bayyana cewa Vini bai lashe kyautar ba, duk da nasarorin da ya samu na lashe gasannin La Liga da Zakarun Turai.
Wannan ya haifar da tawagar Madrid ta ƙauracewa bikin ba da kyautar a birnin Paris, inda aka karrama Rodri da babbar kyautar bajinta a ƙwallo ɓangaren maza.
Zuwa yanzu, Vinicius Jr ya bayyana matsayarsa game da gaza lashe kyautar, cikin wani saƙo da ya wallafa a soshiyal midiya, inda ya ce a shafinsa na X cewa: "Zan sake yin bajinta ninki 10 idan haka ake so na yi. Ba su shirya ba."
Fafutukar kare baƙaƙe
A wani lokaci a Maris, Vinicius ya fashe da kuka lokacin da aka tambaye shi game da zagin launin fata da ake yawan yi masa a yayin wasanni, wanda ake ganin ya kusa kassara ƙarfin zuciyarsa.
Vinicius ya taɓa yin kiran da a karɓe damar karɓar baƙuncin gasar Kofin Duniya ta 2030 daga wajen Sifaniya, idan zagin launin fata ya ci gaba da faruwa a ƙasar, kuma ya nemi a ringa tura masu nuna wariyar launin fata zuwa kurkuku kai-tsaye.
Haka nan, Vini ya yi suna wajen nuna goyon baya ga 'yan wasan da suka fuskanci zagin launin fata, kamar Raphinha da Lamine Yamal da Alejandro Balde na Barcelona, waɗanda suka sha zagi yayin wasan El Clasico da aka yi a makon jiya a gidan Real Madrid.
Jami'an da ke kula da Vini sun faɗa wa Reuters cewa ɗan wasan yana magana ne kan yaƙin da yake kan wariyar launin fata, lokacin da ya yi magana kan zaɓen Ballon d'Or. Tawagarsa ta ce: "Duniyar ƙwallo ba ta shirya karɓar ɗan wasa da ke faɗa da tsarinsu ba."