Ku sanya idanuwa: Abubuwa bakwai dake jan hankali ga Gasar Duniya ta Qatar 2022

Masu goyon bayan kwallon kafa na sauraren a fara Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa ta Duniya ta FIFA ta Qatar 2022. Gasar da za a yi a tsakanin 20 ga Nuwamba da 18 ga Disamba, ita ce gasar kasa da kas ata farko a Duniyar Larabawa.

Ga wasu abubuwa bakwai da wannan gasa za ta rasa a bana:

Messi ya yi bankwana

Mujallar outles star ta Ajantina ta tattauna da Lionel Messi, wanda ya tabbatar mata da cewa gasar cin kofin duniya ta Qatar 2022 za ta zama Gasar Cin Kofin Duniya ta karshe da zai buga. Ya ce tabbas ita ce.

Ya ce, “Ina ci gaba da sauraren ranar fara gasar. Akwai karsashi da karkarwa a lokaci guda. Game da me zai je ya komo.”

Ya kara da cewa, “a gefe guda kuma mun zaku a fara, a daya gefen kuma muna ta tunanin mai zai je ya komo.”

Messi mai shekaru 35 da ya zama daya daga cikin gwarazan kwallon kafa na duniya a yau, zai ci gaba da taka leda a Paris Saint-Germain har nan da watan Yunin 2023, amma akwai yiwuwar a kara wa’adin kwantiragin da shekara daya. Kasancewar ya taka leda a Barcelona baya, ya ce yana tunanin ya zama mai horar da ‘yan wasanta a nan gaba.

Ya ce” Zan so na zama daraktan wasanni a wani mataki. Ban sani ba ko hakan zai kasance a Barcelona ko a wani wajen. Amma idan akwai dama, zan so taimakawa kungiyar.”

Qatar ta samar da karin wajen kwanan baki, ta kara wa’adin zirga-zirgar jiragen kasa

Bloomberg sun rawaito cewa an samarda karin dubunnan dakunan otel, gidajen kwana ga ‘yan kwallo, masu daukar nauyi da maziyarta gasar cin kofin duniya.

Kakakin gwamnatin Qatar ya ce “kasar na kan shirin samar da dakunanan otel dubu 130,000 don gasar, kuma a yanzu akwai dakuna sama da dubu 117,000.”

Kafar yada labaran ta jero zabin wajen sauka da suka hada da gidajen da aka gina, tantuna, gidjen Air bnb da kuma jiragen ruwa guda biyu manya wanda kowanne yana da wajen kwanan mutane dubu 4,000.

‘Yan yawon bude ido da za su halarci gasar ta duniya daga kasashe makota za su dinga zuwa suna fita a rana guda, wanda hakan zai kara yawan jiragen da za su dinga tashi da sauka, godiya ga hadin kan yankin.

Doha News ma sun rawaito cea “Layin dogo na Qatar a koyaushe za su yi aiki da jirage 110 tare da kara zirga-zirga a kowacce rana zuwa awanni 21 don samun damar jigilar fasinjoji.

Makadan Glastonbury za su baiyana

Doha News sun rawaito jaridar The Sun ta rubuta cewa wadnda suka shirya Gasar FIFA ta Duniya sun hayo Arcadia, mamallaka Bukin Glastonbury, don cashewa a yayin gudanar da gasar.

Bukin kade-kade da raye-rayen zai gabatar da shahararrun mawaka a duniya, The Sun ta rawaito cewa “gizo-gizon Glastonbury zasu cashe matuka a kasar.”

Za a nuna rigar Maradona

Gidana Kayan Tarihi na 3-2-1 na Wasannin Olympic na Qatar sun kaddamar da sabon nuna kayayyakin gasar kwallon kafa ta duniya.

Shfin yanar gizon gidan adana kayan tarihin ya yi tsokacin cewa “Maziyarta za su samu damar tuna gasar baya da aka yi ta cin kofin duniya, sannan su ga yadda Qatar ta yi nasarar samun damar karbar bakuncin gasar.”

Daya daga cikin kayan da za a nuna shi ita ce rigar dan kwallon kafar Ajantina Diego Maradona da ya jefa kwallonsa ta “Hannun Abun Bauta” a yayin karawar su da Ingila a 1986. Doha News sun rawaito cewa Gidan adana kayan tarihin ya ari rigar ruwan bulawadda aka sayar a yayin wani gwanjon kayayyakş a watan Mayu kan kudi dala miliyan 9.3.”

Sohail da Soraya, panda jakadun China ga Gasar ta Duniya

A ranar 26 ga Satumban 2022 ne China ta sanar da za ta aika da dabbobin panda guda 2 masu suna Sohail da Soraya zuwa Doha a watan Oktoba tun kafin fara gasar ta duniya.

Doha News ya sanar da cewa “Duk da ba su iya samun damar halartar gasar ta duniya ba, kamfanunnukan China sun bayar da babbar gudunmowa ga manyan aiyukan da suka shafi gasar.”

Wadannan panda wani bangare ne na diplomasiyyar siyasa ta China, dake nuna alakarta ta kusa da kawayenta. Kafar yada labaran ta yi tsokacin cewa wannan al’ada na komawa ga Sarauniya Wu wadda ta aika da panda zuwa Japan a karni na bakwai, kuma a lokacin Mao Zedong aka dawo da wannan al’ada a gwamnatance.

Wakar Kofin Duniya ta Larabci ‘Arhbo’ ta yi tashe

Wakar ‘Arhbo’ da aka saki a watan Satumba saboda gasar ta FIFA ta Duniya ta samu kusan masu sauraro miliyan 16 a YouTube.

Doha News sun bayyana wakar a matsayin “Tana kan harshen kusan duk wani Balarabe.. godiya ga amo da kafiyarta dake jan hankali... ta samu karbuwa sosai bayan an sake ta.”

Doha News sun kuma rawaito cewa waka da bidiyon suns amu bayar da umarni daga dan kasar Qatar bai basira Mohamed Al Ibrahim, kuma an samar da ita a wani dakin shirye-shirye a Doha.

Masu fasa matasa daga Gabas ta Tsakiya ne suka rera wakar, a cikin wakar ana ganin Nasser Al Kubaisi, mawakin Qatar matashi, Mawakin Saudiyya Ayed Yousef wanda na daga cikin alkalan gasar wakoki ta Saudiyya. Mai taken “Ka kayar da ni idan za ka iya” da kuma Haneen Hussain wanda ya rubuta wakar ‘Bravo Alek’ tare da Abdelaziz Lewis, da Badr Al Shu’aibi wanda ya samu makalla sama da miliyan 117 a YouTube.

Mareran Sarewa na Qatar za su bayyana

Idan ka ziyarci Doha a yayin Gasar FIFA ta Duniya, akwai yiwuwar ka ga wajen da ake rera sarewa ta Watar a bainar jama’a.

Maimakon baje-kolin da aka saba gani, adannan marera za kuma su rare wakokin ‘yan kwallon kafa na duniya, wakokin gargajiya na yankin Gulf, Wakokin Larabawa da ma wasu sabbin waken sarewar, kamar yadda Daraktan Kungiyar Kurt Meister ya bayyana ga Doha News.

Ya ce, “Mun kammala shirye-shiryen ga shahararrun wakoki da kuma mafiya shahara na kwallon kafa daga kasashen duniya daban-daban.”

TRT Afrika da abokan hulda