Joshua na fatan zama zakaran duniya a gasar dambe a karo na uku, amma sai in har ya yi nasara a kan Ngannou

A ranar Juma'a mai zuwan nan za a yi wani gagarumin wasan dambe tsakanin shahararren ɗan damben nan ɗan Nijeriya da Birtaniya Anthony Joshua da kuma wani shahararren Francis Ngannou ɗan ƙasar Kamaru a ƙasar Saudiyya.

Ƴan damben za su fafata ne a zagaye 10 a babban birnin Saudiyya, Riyadh.

Joshua na fatan zama zakaran duniya a gasar dambe a karo na uku, amma sai in har ya yi nasara a kan Ngannou mai shekara 34 tukunna.

Idan har ya yi nasara a kan Ngannou, to a lokacin ne zai fara jiyo ƙamshin shiga gasar damben boxing ta duniya International Boxing Federation (IBF), inda zai ffaata da ɗan ƙasar Crotia da aka ayyana a matsayin ɗan damben duniya Filip Hrgovic.

Sai dai kuma Ngannou ba kanwar lasa ba ne a wasan dambe, musamman idan aka kalli irin rawar da ya taka a fafatawarsa da Tyson Fury a watan Oktoban 2023. Ngannou ya kusa samun nasara mafi girma a tarihin gasar damben boxing.

Duk da cewa Fury ne ya samu maki mafi yawa, sai da ɗan damben Kamarun ya kai Fury ƙasa a zagaye na uku.

Dukkan ƴan damben sun yi alkawarin yin wasa na ban mamaki. Hoto: Getty Images 

Idan har Ngannou ya yi nasarar ban mamaki a kan Joshua to hakan zai ƙarfafa matsayinsa na gwarzo.

An zaƙu ƙwarai don ganin wannan arangama tsakanin Joshua da Ngannou don ganin yadda za ta kaya.

Rikicin zai kasance wasan damben ƙwararru. An shirya fafatawar za ta kasance zagaye 10 a tsawon mintuna uku kowane zagaye. Kowane ɗan wasan na iya yin nasara ta hanyoyi da dama.

Babu ɗan wasan da ke riƙe da wani kambi, don haka babu wanda za a ce zai ci gaba da riƙe kambin ko kuma ya rasa shi a ƙarshen wasan.

Dama Joshua ya rasa kambinsa na WBA da WBO da kuma IBF, bayan da sau biyu yana shan kaye a hannun Oleksandr Usyk a 2021 da 2022.

Akwai lada mai tsoka a wannan wasan, inda Joshua zai iya samun dala miliyan 50 idan ya yi nasara, shi kuma Ngannou zai samu dala miliyan 20 idan shi ne ya yi nasara.

TRT Afrika