Tawagar kwallon kafar Nijeriya, Super Eagles, ta fadi daga matsayi na 35 zuwa na 40 a sabon teburin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar.
FIFA ta wallafa bayani kan sabon teburin ne a shafinta na intanet ranar Alhamis.
Kazalika tawagar ta Nijeriya ta yi kasa zuwa mataki na shida a nahiyar Afirka.
Sabon teburin ya nuna kasashe da kuma matsayinsu bisa iya murrza ledarsu.
Jadawalin ya nuna cewa Ajentina ce kasa ta daya a duniya a fagen tamaula yayin da kasar Faransa take biye da ita.
Kasar Morocco da ta kai wasan kusa da na karshe a gasar Kofin Duniya ke kan gaba a Afirka kuma tana ta 11 a duniya.
Kasar Senegal dage rike da Kofin Afrika ce ta biyu a nahiyar yayin da take ta 18 a duniya.
Ita kuma kasar Tunisiya ta koma ta uku a Afrika yayin da take ta 18 a duniya.