Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA, ta amince wa alkalan wasa 30 daga Nijeriya su yi aiki a wasanni daban-daban na duniya a shekara mai zuwa, kamar yadda Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya NFF ta sanar.
Mutanen sun haɗa da rafari ɗin ƙwallon ƙafa 11 da mataimakan rafari 11 da rafari ɗin ƙwallon yashi huɗu da kuma rafari na ƙwallon futsal huɗu, kamar yadda kafafen watsa labaran Nijeriya suka rawaito.
Wasu daga cikin jami'an da ke kan sabon jerin na FIFA sun taɓa kasancewa a cikin jerinta na shekarar 2019.
Ba a samu wasu bayanai na gasannin da jami'an za su yi aiki a cikinsu ba.
Nijeriya na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen Afirka da ke buga ƙwallo, amma yawancin rafari ɗinta ba sa samun shiga manyan gasanni na duniya.
Babu alkalin wasa ko ɗaya daga Nijeriya da aka sanya a cikin jami'ai 85 da aka amincewa su yi aiki a Gasar Kofin Nahiyar Afirka da za a fara ranar 8 ga watan Janairu a Cote d'ivoire.
Kwanan nan Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya ta ɗauki matakin sake horas da alkalan wasa saboda aikin ya ƙara yin amfani da fasaha.