Tawagar maza ta kwallon kwando 'yan kasa da shekara 19 ta Turkiyya ta doke takawarta ta Amurka da ci 84-70 a gasar FIBA ta Duniya, inda ta zo mataki na uku.
A gasar da aka yi a Debrecen, Hungary, ranar Lahadi, Turkiyya ta fafata da Amurka - kasar da ta fi yin nasara a gasar inda ta dauki kofin kalubale sau 8.
"Ina taya murna ga 'yan wasanmu da masu horar da su da suka taimaka wajen samun wannan nasara," in ji Ministan Matasa da Wasannin Turkiyya Osman Askin Bak.
Ya kara da cewa: "Ina fata za a ci gaba da samun nasara irin ta wadannan matasa 'yan uwana, wadanda suka zo na uku a duniya bayan sun zage dantse da kuma jajircewa, kuma zai sa nan gaba mu samu kwarin gwiwa."
Tawagar Turkiyya ta soma wasan da kafar dama, inda ta gama zagayen farko da ci 25-18, sannan ta yi nasara da 39-33 yayin da aka tafi hutun rabin lokaci.
Ta samu tagulla karo na biyu a FIBA
Turkiyya ta lashe tagulla a karo na biyu a tarihin gasar, bayan ta zo ta uku a 2015.
'Yan wasan Turkiyya da suka taka rawar gani sun hada da Tan Yıldızoğlu wanda ya samu maki 20, ya taimaka aka samu 8; Berke Büyüktuncel ya samu maki 19, ya taimaka aka samu 5; Özgür Cengiz ya ci maki 11, ya taimaka aka samu 5; Samet Yiğitoğlu ya ci maki 10 da kuma 11da ya taimaka aka samu.
Amurka ta sha kashi duk da maki 15 da dan wasanta Dylan Harper ya samu da kuma maki 12 da takwaransa Cody Williams ya ci.