An saki ɗan ƙwallon Isra'ila Sagiv Jehezkel a ranar Litinin, bayan da aka tsare shi saboda abin da ya aikata a yayin wasan Turkiyya na Super Lig.
An tsare Jehezkel ne bayan da ya zura ƙwallo a raga a wasan Antalyaspor-Trabzonspor, kan "tuncura jama'a su nuna ƙiyayya" a bisa aniyarsa ta goyon bayan cin zalin da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa tun ranar 7 ga Oktoba.
A cikin bayanin da ya yi wa ‘yan sanda, Jehezkel ya ce kafin ya shiga filin, ya rubuta “kwana 100” da kuma “07.10” a kan farin bandejin da ke wuyan hannunsa na hagu, inda ya ji rauni sannan ya zana Tauraron Dauda, a cikin dakin da 'yan wasa ke shiryarwa.
Ya jaddada cewa babu wani dan tawagarsa ko ɗaya daga cikin ma'aikatan a lokacin da ya aikata hakan.
"Burina shi ne na jawo hankali kan cikar kwana 100 da fara yakin nan tsakanin Hamas da Isra'ila," in ji Jehezkel.
"Bayan awa biyu da kammala wasan, sai na fahimci cewa abin da na yi a lokacin wasan ya watsu a shafukan sada zumunta tare da jawo ka-ce na-ce," ya faɗa.
“Ina matukar ba da hakuri ga daukacin al’ummar Turkiyya kan wannan abin da na yi a lokacin wasan. Na yi nadama. Ban yi nufin tsokanar kowa ba. Ni kuma ban yi tsammanin hakan zai iya haifar da irin wannan martanin ba."
Kungiyar Antalyaspor ta sanar da cewa an fitar da Jehezkel daga tawagar.