Ɗan Nijeriya Lookaman ne ya zama gwarzon CAF na 2024. / Hoto: CAFonline

Gwarzon ɗan wasan Afirka: Ademola Lookman

Wanda ya lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Afirka, Ademola Lookman, dan wasan gaba ne na tawagar Nijeriya, wanda ya taka rawar gani a gasar AFCON da Nijeriya ta zo ta biyu a farkon shekarar nan.

Lookman ya kafa tarihin cin ƙwallaye uku rigis a wasan ƙarshe na gasar Europa da ƙungiyar da yake buga wasa ta Atalanta ta Italiya ta lashe, bayan doke Bayer Leverkusen da ci 3-0.

Gwarzuwar 'yar wasan Afirka

Barbra Banda 'yar Zambia ce ta gwarzuwar 'yar ƙwallon ƙafa rukunin mata a Afirka ta CAF a shekarar 2024. Barbra Banda mai shekaru 24 'yar wasan gaba ce kuma kyaftin ɗin tawagar ƙasar Zambia.

Gwarzuwar tawaga

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Ivory Coast ce gwarzuwar tawagar ƙasa a rukunin maza a bana. Tawagar ce dai ta lashe kofin ƙasashen Afirka na AFCON 2023 da aka yi a watan Janairun shekaran nan a can Ivory Coast ɗin.

Kamar a bara, tawagar Super Falcons ta Nijeriya ce ta lashe kyautar gwarzuwar tawagar ƙasa ta mata a shekarar 2024, bayan doke tawagogin Morocco da Afrika ta Kudu.

Gwarazan koci

Kocin tawagar Ivory Coast ta maza, Emerse Fae shi ne gwarzon kocin Afirka na bana. Fae ya fara gasar AFCON ta bana a matsayin mataimakin koci Jean-Louis Gasset wanda ya yi murabus ya bar Fae wanda shi ya kai tawagar zuwa lashe kofin.

Lamia Boumehdi ce ta lashe kyautar gwarzuwar koci rukunin mata a Afirka a 2024. Lamia 'yar asalin Morocco ce, kuma ita ta jagoranci TP Mazembe wajen lashe kofin zakarun nahiyar Afirka na mata, bayan lashe kofin mata na Congo DR.

Gwarzuwar ƙungiya

Al Ahly ta Masar ce gwarzuwar ƙungiyar ƙwallo a nahiyar Afirka a 2024, inda ta lashe kyautar a karo na uku a jere a bana, yayin da ƙungiyar TP Mazembe ta zama gwarzuwar ƙungiyar mata ta Afirka a bana.

Gwarazan masu tsaron gida

Gwarzon mai tsaron gida na Afirka rukunin maza shi ne Ronwen Williams, ɗan asalin Afirka ta Kudu, wanda ke tsaron gidan tawagar maza ta Afirka ta Kudu.

Chiamaka Nnadozie ta Nijeriya ce ta lashe gwarzuwar mai tsaron gida ta Afirka rukunin mata.

Mai shekaru 24, Chiamaka haifaffiyar jihar Imo ce a kudu maso gabashin Nijeriya, kuma tana buga wa tawagar mata ta Nijeriya da kuma ƙungiyar Paris FC a matsayin mai tsaron gida.

Matasan 'yan wasa

Gwarzon ɗan wasan Afirka a bana shi ne Lamine Camara, ɗan Senegal da ke buga wa AS Monaco a Italiya. Camara ɗan wasan tsakiya ne mai shekaru 20 da yake buga wa tawagar ƙasar Senegal.

A rukunin mata, Doha El Madani 'yar asalin Morocco ce ta lashe kyautar gwarzuwar matashiyar 'yar ƙwallo, saboda ƙoƙarinta a gasar zakarun nahiyar Afirka ta CAF.

TRT Afrika