Bukayo Saka dan asalin Nijeriya ne, amma yana buga wa tawagar kwallon kafa ta Ingila wasa : Hoto/Reuters

Dan wasan gaban Arsenal, wanda ya cika shekara 22 a ranar Talata, ya kasance wanda magoya-bayan tawagar kwallon kafa ta Ingila suka fi kada wa kuri'a a matsayin dan wasan kasar da ya fi iya taka leda a karo na biyu cikin shekaru biyu.

Bukayo Saka wanda asalinsa dan jihar Kwara ne da ke Nijeriya, shi ya samu lambar yabon dan wasan Ingila da ya fi iya taka leda a kakar da ta gabata, wato kakar 2021-22.

Dan wasan tsakiya Jude Bellingham ne na biyu a cikin wadanda aka fi zaba yayin da keftin din Ingila kuma wanda ya fi zura mata kwallo a raga a tarihi Harry Kane ya zo na uku.

Saka ya zura wa Ingila kwallo bakwai a raga cikin wasanni 10 a shekarar da ta gabata, ciki har da kwallo uku da ya fara zurawa a wasa daya a lokacin da Ingila ta doke North Macedonia da ci 7-0 a Old Trafford.

A gasar kwallon kafa ta duniya da aka yi a Qatar a shekarar 2022, ya zura wa Ingila kwallo sau uku, inda ya zura kwallo biyu a ragar Iran a wasan da Ingila ta doke Iran 6-2, kuma ya zura kwallo daya a ragar Senegal a wasan da Ingila ta doke Senegal 3-0.

Saka, wanda aka bai wa lambar yabon matashin dan wasan da ya fi iya kwallo a kulob dinsa Arsenal a kakar da ta gabata ya zura wa ingila kwallaye 11 a raga cikin wasanni 28 .

Kazalika dan wasan na cikin ‘yan wasan da kocin Ingila Gareth Southgate ya gayyata domin wasan neman shiga gasar cin kofin Turai inda Ingila za ta kara da Yukrain.

TRT Afrika