Sadi Mane ya bi sahun wasu 'yan wasan da suka sayi kulob na kansu irin su Ronaldo Dilma:Hoto/Getty Images

Shahararren dan wasan Senegal wanda yake taka leda a Kungiyar Al-Nassr ta kasar Saudiyya ya sayi kungiyar kwallon kafa ta Bourges 18 da ke kasar Faransa.

Magajin Garin Bourges Yann Galut ne ya sanar da hakan yayin wani taro da ya yi da manema labarai a hedikwatar kungiyar a ranar Laraba.

Sai dai kungiyar Bourges 18, wacce take wasa a rukuni na hudu a Faransa, ba ta sanar da kudin da ya saye ta ba.

An kafa kungiyar ne a shekarar 2021 bayan da kungiyoyin Bourges Foot da kuma Bourges 18 sun dunkule zuwa kungiya daya.

Al-Nassr ta sayi Sadio Mane a kan Yuro miliyan 40 a shekara daga kungiyar Bayern Munich ta Jamus.

An shaidi Sadi Mane da taimaka wa mutane a kasarsa, Senegal:Hoto/Getty Images

Kawo yanzu Mane ya buga wa Al-Nassr wasanni 13 a kakar bana, inda ya zura kwallaye bakwai sannan ya taimaka aka zura biyu.

TRT Afrika