Babbar nasara: Turkiye ta lashe gasar Kwallon Kafa ta Masu Kafa Daya ta Duniya

Turkiye ta lashe Gasar Kwallon Kafa ta Masu Kafa Daya ta Duniya ta 2022, inda ta doke Angola dake rike da kofin da ci 4 da 1.

A ranar Lahadi ne ‘yan wasan Turkiye suka samu nasarar daga kofin na duniya, bayan da a zagayen farko ake da 1 da 1 da Omer Guleryuz na Turkiye da Adao na Angola suka jefa a raga.

Rahmi Ozcan ya jefa kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida inda hakan ya sanya Turkiye zama a kan gaba.

Serkan Dereli ya sake jefa kwallo, inda Turkiye ta rama abun da Angola ta yi mata a wasan karshe na shekarar 2018.

Shugaban Kasar Turkiye Recep Tayyip Erdogan ya halarci kallon wasan na karshe inda d kansa ya mikawa ‘Yan wasan kofin.

A sakon da ya fitar ta shafin Twitter, Shugaba Erdogan ya ce “Ina taya murna sosai ga Kungiyarmu ta Kwallon Kafa ta Masu Kafa Daya, saboda kokari, jajircewa da nasarar da suka samu.”

Tıun da fari a ranar Lahadi, Uzbekistan ta doke Haiti a neman na uku.

Nasarar Turkiye

Kungiyar Masu Kafa Daya ta Kwallon Kafa ta Turkiye ta isa ga wasan karshe a Gasar Kofin Duniya bayan doke Uzbekistan da ci 1 da 0 a ranar Juma’a.

Omer Guleryuz ne ya jefa kwallon daya mai ban haushi a mintunan farko, wadda ita kadai aka jefa a wasan a filin wasanni na Vodafone Park..

A gasar Masu Kafa Daya ta Kwallon Kafa ta Duniya da aka gudanar a Mekziko a 2018, Turkiye ta yi rashin nasara a hannun Angola a bgun daka kai sai mai tsaron gida da ci 5 da 4.

Kafin fara buga wasa a gasar duniya, ‘yan wasan na Turkiye sun nuna jarumta a wasannin nakasassu, wasannin da masu nakasa suke bugawa, da suka hada nakasa ta jiki ko ta kwakwalwa, kuma sun lashe gasar Turai.

A 2017, Turkiye ta lashe gasar Turai bayan ta doke Ingila da ci 2 da 1 a wasan karshe a gaban masu kallo dubu 40,000 da suka cika filin wasa na Vodafone Park dake İstanbul.

AA