Gasar Zakaru ta Masu Ninkaya gasa ce ta duniya da ake yin wasannin da suka shafi ruwa kamar ninkaya da zamiya. Photo: AFP

Wani mai wasan ninkaya dan Tunisiya Ahmed Ayoub Hafnaoui ya yi nasarar cin kambin zinare a Gasar Zakarun Wasan Ruwa ta Duniya a Japan.

A gasar ta mita 800 Hafnaoui ya zama zakara, in da ya wuce dan Australiya Samuel Short da ya ci kambin azurfa, sannan Bobby Finke na Amurka ya yi na uku da kambin tagulla.

Wannan ne karo na farko da Hafnaoui mai shekara 20 ya ci kambin zinare a Gasar Ninkaya ta Duniya ta mita 800. Zai kuma fafata a gasar mita 1500 ta zakaru da za a yi a Fukuoka, Japan.

Gasar Zakaru ta Masu Ninkaya gasa ce ta duniya da ake yin wasannin da suka shafi ruwa kamar ninkaya da zamiya.

Nasara a tarihi

A lokacin da yake dan shekara 18, Hafnaoui ya ci kambin zinare a gasar mita 400 a Gasar Wasannin Olympic da aka yi a birnin Tokyo na Japan a 2020.

Hafnaoui ya zama dan Tunisiya na farko da ya zama zakara a gasar Olympic tun bayan da Oussama Mellouli ya ci kambin zinare a gasar mita 1500 a Gasar Olympic da aka yi a birnin Beijing na China a 2008.

Sannan a lokacin da yake dan shakera 15 ya ci kambin tagulla a Gasar Ninkaya ta Afirka ta mita 1500 da aka yi a Aljeriya, sannan ya ci kambin azurfa a gasar mita 4x200.

TRT Afrika