Mesut Ozil Ya lashe kofin FA na Ingila sau hudu a Arsenal

Tun lokacin da tsohon dan wasan Arsenal, Mesut Ozil, ya sanar da cewar ya yi ritaya daga wasan kwallon kafa ake ta tattauna akansa.

Ga kadan daga cikin abubuwan da ya kamata ka sani game da dan wasan:

Tsohon dan wasan Nijeriya, Jay Jay Okocha, ya kasance dan wasan da Mesut Ozil ya fi so a lokacin da yake yaro.

Dan wasan, mai shekara 34, ya fara taka leda ne a Schalke 04 ta Jamus amma daga bisani ya koma Werder Bremen.

Salon taka ledarsa ya sa an gayyace shi tawagar ‘yan wasan Jamus inda ya yi wasa a gasar kwallon duniya ta shekarar 2010 inda tawagar ta zama ta uku a duniya.

undefined (Others)

Bayan wata daya da kamala gasar, Mesut ya rattaba hannu kan kwantiragi da Real Madrid ta Sifaniya inda ya taka leda tsawon shekara uku kuma ya samu damar cin kofin la Liga da Super Cup na Sifaniya.

Ya buga wasanni 105 a Real Madrid kuma ya zura kwallaye 19 a raga.

Ya koma Arsenal a shekarar 2013 inda ya taimaka wa kulob din na Ingila lashe kofin FA har sau hudu.

Ozil na cikin tawagar Jamus da ta lashe kofin duniya a shekarar 2014.

A shekarar 2021 ya koma Fernabache daga Arsenal. Daga baya ya koma taka leda a Istanbul Basaksehir kafin ya sanar da murabus dinsa daga wasan kwallon kafa.

undefined (Others)

Ozil ya buga wasanni 645 wa kungiyoyin kwallon kafa da tawagar kwallon kafa inda ya zura kwalaye 114 a raga.