Samuel Eto'o
Dan wasan gaba dan kasar Kamaru Samel Eto’o ne dan wasan Afirka da ya fi kowa daga kofuna. Tsohon dan wasan na Barcelona da Inter ya samu kambin Zakaran Dan Wasan Gasar Zakarun Turai har sau uku: Sau biyu da Barcelona a kakar wasanni ta 2005/2006 da 2008/2009, sai sau daya da Inter Milan a kakarw asanni ta 2009/2010. Eto’o ya zama dan Afirka da ya fi kowa jefa kwallaye a matsakin C1 inda ya ci kwallaye biyu. Dan wasan na Kamaru ya zama dan Afirka na biyu mafi yawan buga wasannin Gasar Zakarun Turai, ya buga wasanni 81 da nasarori 33.
Didier Drogba
Didier Drogba dan kasar Kotdebuwa, shi ne dan Afirka da yafi kowanne samun kambi a Gasar Zakarun Turai tare da wasanni 89 da kwallaye 42 inda yake gaba da Samuel Eto’o. Tsohon dan wasan kungiyar Chelsea ya lashe Gasar Zakarun Turai a 2012 tare da masu shudayen kaya, bayan ya taka babbar rawa a nasarar da suka yi kan Bayern Munich. Drogba bai samu damar buga wasannin C1 da Olympique de Marseille ba, amma kuma ya samu damar yin hakan bayan ya koma kungiyar Galatasaray ta Türkiye.
Mohamed Salah
Dan kasar Masar mai shekaru 30 ya buga wasanni sama da 80 a Gasar Zakarun Turai, ya jefa kwallaye 40 a tsakanin zaman sa a FC Basel, Chelsea, AS Roma da Liverpool. A yanzu shi ne dan Afirka da ya fi kowa kwallaye a C1, inda yake baya da kafa hudu da mai rike da kambin, Didier Drogba. Mohamed Salah da ya lashe Gasar Zakarun Turai tare da Jajaye a shekarar 2019, ya buga wasannin karshe na C1. Kafin ya yi ritaya, dan kasar Masar zai iya wuce dan kasar Kotdebuwa da yawan kwallaye da wasanni. Za a ci gaba.....
Sadio Mane
A yanzu yana taka leda a kungiyar Bayern Munich, dan wasan dan kasar Sanagal na kuma buga wasanni a gasar Zakarun Turai. Abokin dan wasan Masar Salah a Liverpool. Sadio Mane ba shi ba shi da alkaluma da yawa kamar na tsohon abokin wasansa. Amma sabon dan wasan na Bayern Munich ya yi shuhura a lokacin da Jajaye suka ba shi kambi a 2019, inda ya jefa kwallaye hudu, ya kuma bayar da taimako aka jefa biyu. Kari kan alkaluman, dan wasan na Sanagal ya kware wajen taka leda da yanka a filin kwallo.
Nwankwo Kanu
Dan wasan gaba dan Najeriya ya lashe Gasar Zakarun Turai a shekarar 1995 tare da kungiyar Ajax Amsterdam. Kasancewar sa ya buga wasanni a wasanni 60 na C1, dan wasan mai tsayin mita 1 da santimita 96 ya kuma lashe gasar Kasashen Afirka a 1996 da 1999. Ga matasan da ba za su iya tuna Kanu ba, dan wasan gaba ne dake da kwarjini wanda ya kawo martaba ga kungiyoyi da dama a Gasar Premier ta Ingila a tsawon shekaru 14.
Riyad Mahrez
Dan wasan dan kasar Aljeriya bai taba lashe Gasar Zakarun Turai ba, amma ya bayar da babbar gudunmowa ga rawar ganin da Manchester City ta yi a 2021. A wasan karshe Chealsea ta yi nasara a kansu, ‘yan wasan Manchester City sun samu nasara kan Paris Saint-Germain a wasan semi final saboda jajircewar Mahrez. Saboda jefa kwallaye 17 a wasanni 47 na C1, dan wasan na Aljeriya na da manufar kara alkalumansa a karkashin allon ‘Pep Guardiola’ na Manchester City.
Emmanuel Adebayor
Yayinda dan wasan dan kasar Togo bai taba lashe babban kofi ba, amma yana amsa bukatar kungiyoyin Turai, ya yi nasarar rigunan manyan kungiyoyi kamar real Madrid, Arsenal, AS Monaco da Manchester City. Dan wasan gaba mai kyau, Adebayor ya jefa kwallaye 13 a Gasar Zakarun Turai.
George Weah
A shekarar 1995, Ballon d’Or bai buga wasanni a Gasar Zakarun Turai ba. Dan wasan Paris Saint-Germain a wancan lokacin, AC Milan ta doke shi a wasan kusa da na karshe na gasar C1,kungiyar da yakoma bayan kakar wasannin. Gaba daya dai, ya jefa kwallaye 14 a wasanni 22 na C1--- wannan adadi ne mai kyau ta fuskar jefa kwallaye.