Rahotanni da ke fitowa daga kasar Italiya game da dan kwallon kafa na kungiyar Napoli da ke buga wasa a gasar Serie A, wato Victor Osimhen, suna nuna cewa hazikin dan wasan ya goge duka hotunansa a rigar kulob din daga shafinsa na Instagram.
Hakan na zuwa ne bayan da shafin TikTok na kulob din na Napoli ya wallafa wani faifan bidiyon da ke muzanta dan wasan, bayan da ya zubar da bugun daga kai sai gola, a wasan da Napoli ta buga da kungiyar Bologna ranar Lahadi, wanda aka tashi babu mai cin ƙwallo.
Daya daga cikin bidiyon ya nuna Osimhen a matsayin dan kwakwa, tamkar dai ana nuna cewa kwakwalwarsa ko kuma shi din kwakwa ne, wanda ake ganin a matsayin zagi da nuna kyamar launin fata.
Tuni dai aka ruwaito cewa kulob din ya goge wannan bidiyo daga shafinsa na TikTok, bayan da ya sha suka daga, sakamakon fassara abin a matsayin nuna bambanci da rashiin daraja ga babban dan wasan da ya kamata su yi takama da shi.
Victor Osimhen dan Nijeriya ne kuma gwarzon dan wasa ne da ya jagoranci ciyo wa Napoli kopin Serie A, a bara. Tuni dai aka ruwaito wakilin dan wasan ya yi barazanar cewa dan wasan zai iya daukar matakin shari'a kan kulob din nasa.
Wakilin Osimhen, Roberto Calenda ya ce, "Abin da ya faru a shafin TikTok na Napoli ba abu ne da za a amince da shi ba. Wallafa bidiyo mai muzanta Victor, duk da an goge shi, ya cutar da dan wasan.... Muna da ikon daukar matakin shari'a don kare mutuncin Victor."
Wani dan jarida mai fashin baki kan wasanni, Kaveh Solhekol ya fada a wata hira da aka wallafa a shafin X na Sky Sports Football, ya bayyana cewa "Osimhen dan wasa ne da ya kamata Napoli ta daraja."
"Shi ya taimaka musu suka ci kofin Serie A, shekaru 30 bayan sun taba cin kofin lokacin da shahararren dan wasan nan Diego Maradona ya jagorance su", in ji Solhekol.
Takkadama tsakanin Osimhen da kungiyarsa ta Napoli ta janyo a yanzu an fara tattaunawa kan makomar dan wasan, musamman ganin har yanzu kulob din bai fito ya nemi afuwar dan wasan ba.