A ranar Juma'a 24 ga watan maris ne tawagar kwallon kafa ta Nijeriya Super Eagles, za ta kara da tawagar kwalalon kafa ta Guinea Bissau cigaba da wasannin neman shiga gasar cin kofin Afirka da za a yi a Ivory Coast.
Za a yi wasa ne a filin kwallon kafa na Moshood Abiola da ke Abuja, babban birnin Nijeriya.
Tawagar kwallon kafar Nijeriyar tana saman teburin rukunin A da maki shida bayan da ta yi nasara a wasanni biyu.
Ita kuwa tawagar Guniea-Bissau tana ta biyu a teburin rukunin A din da maki hudu bayan nasararta a wasa daya tare da tashi canjaras a wasa daya.
Watan Janairun bara ne karo daya tilo da tawagar ta Nijeriya ta taba haduwa da tawagar kwallon kafa ta Guinea-Bissau a Gasar Cin Kofin Afirka (AFCON) inda ta doke ta da ci biyu da nema.
Rahotanni daga Nijeriya sun ambato kyaftin din Nijeriya, Ahmed Musa, wanda yake taka leda a kulob din Turkiye, Sivasspor, yana cewa tawagar ta Super Eagles za ta faranta wa ‘yan Nijeriya rai a wasan da za a yi a Abuja.
Cikin ‘yan wasan da aka gayyata don fafatawar akwai Zaidu Sanusi da ke taka leda a FC Porto da Victor Osimhen wanda shi ya fi zura kwallo a raga a gasar Seria A ta kakar bana inda ya zura kwallo 21 a raga.
Hari la yau Osimhen din shi ya fi zura kwallo a raga a wasannin neman shiga Gasar Cin Kofin Afirka (AFCON 2023) inda ya zura kwallo 5 a raga, a wasannin neman shiga Afcon da aka yi kawo yanzu.
A bara ne Super Eagles ta buga wasanta ta karshe a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja inda ta tashi da 1-1 da tawagar kwallon kafar Black Stars ta Ghana.
Wannan lamari ya sa Nijeriyar ta kasa samun gurbin shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka yi a Qatar a bara (Qatar 2022).