Napoli ta lashe Kofin Serie A karon farko a shekara 33 a yayin da suka yi canjaras da Udinese a wasan da suka fafata a Dacia Arena.
Wannan wasa ya sanya magoya bayan kungiyar cikin matukar murna.
Dan wasan Nijeriya Victor Osimhen ne ya farke kwallon da Sandi Lovric ya ci su a minti na 52.
Sun dauki Kofin ne karon karshe a 1990 tare da Diego Maradona.
Kocin Napoli Luciano Spalletti ya ce sun ga tasirin Maradona a "nasarar" da suka samu.
"Napoli, wannan Kofi naku ne," in ji shi. "Akwai mutanen da za su samu saukin matsalolin da ke damunsu idan suka tuna wannan rana. Ya dace wadannan mutane su ji dadi a rayuwarsu."
TRT Afrika da abokan hulda