A 2022, Pogba ya sake komawa Juventus amma ba kasafai yake buga wasa ba sakamakon raunukan da yake fama da su./Hoto:Reuters

An dakatar da dan wasan Juventus da Faransa Paul Pogba daga kwallon kafa bayan an gano yana shan abubuwan kara kuzari.

"Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta sanar a yau Litinin, 11 ga watan Satumba, 2023, cewa Paul Labile Pogba ya karbi takardar dakatarwa daga kotun yaki da shan kayan kara kuzari bayan gwajin da aka yi masa ranar 20 ga watan Agusta," in ji kungiyar.

"Kungiyar tana da damar yin nazari kan mataki na gaba," a cewar sanarwar.

An dakatar da Pogba ne bayan Juventus ta doke Udinese ranar 20 ga watan Agusta a wasan da aka bar shi a benci.

Pogba, wanda ya lashe Kofin Duniya a 2018, shi ne dan wasa mafi tsada lokacin da ya bar Juventus zuwa Manchester United a 2016. United ta biya €105m ($116.4m) domin sayen Pogba daga Juventus.

Ya taimaka wa Manchester United wajen cin Kofin UEFA Europa na 2017.

A 2022, Pogba ya sake komawa Juventus amma ba kasafai yake buga wasa ba sakamakon raunukan da yake fama da su.

AA
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince