Osimhen ya ji rauni ne a wasan sada zumunta da Nijeriya ta yi da Saudiyya ranar 13 ga watan Oktoba, wanda aka tashi da ci 2-2./Hoto:AFP

Kocin Napoli FC Rudi Garcia ya bayar da sanarwar dawowar dan wasan Nijeriya Victor Osimhen bakin fama, bayan ya yi jinyar kusan wata guda sakamakon raunin a ya ji a cinya.

Osimhen zai koma atisaye a yau Laraba amma ba zai fafata a wasan da tawagarsu za ta yi da Union Berlin na Gasar Zakarun Turai a Rukunin C, kamar yadda Garcia ya shaida wa taron manema labarai ranar Talata.

Osimhen ya ji rauni ne a wasan sada zumunta da Nijeriya ta yi da Saudiyya ranar 13 ga watan Oktoba, wanda aka tashi da ci 2-2.

Garcia ya ce Osimhen zai zauna a benchi har sai lokacin karawar da za Napoli za ta yi da Real Madrid ranar 29 ga watan Nuwamba a Rukunin C.

A halin yanzu Napoli tana mataki na biyu a Rukunin C a Gasar Zakarun Turai, inda take bayan Real Madrid da maki uku, don haka babu shakka fafatawar za ta yi zafi.

TRT Afrika