Hukumar da ke kula da harkokin kwallon kafar Turai UEFA ta dakatar da Juventus daga buga gasar Turai a kakar wasanni mai zuwa saboda karya dokokin wasanni.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a UEFA ta ce za kuma ta sanya tarar Yuro miliyan 20 kan Juventus.
An sanya wa kungiyar haramcin ne bayan ta saba wasu dokokin UEFA kan lasisi da kayyade kashe kudi, yayin da ita ma Chelsea za ta biya Yuro miliyan 10 saboda ta mika bayanan kashe kudinta da ba su cika ba, a cewar UEFA.
A watan Disamba ne bangaren da ke kula da batun kashe kudi na UEFA (CFCB) ya kaddamar da bincike a kan Juventus, watanni bayan kungiyar ta shiga cikin kungiyoyi takwas da suka cimma matsaya da UEFA bayan sun kasa bin tanade-tanaden da hukumar ta gindaya.
UEFA ta ce za ta kara sanya tarar Yuro miliyan 20 kan Juventus.
"A cikin wannan kudi, kungiyar za ta biya Yuro miliyan 10 idan ba ta bi ka'idoji ba kan bayanai na kashe kudinta na shekarar 2023 da 2024 da kuma 2025," in ji UEFA.
Juventus, wadda za ta buga wasan neman gurbin shiga gasar Conference League bayan ta kammala gasar Serie A a matsayi na bakwai a kakar da ta wuce, ta ce ba za ta daukaka kara ba amma kuma kungiyar ta ce ba ta aikata ba daidai ba.
"Ba za mu bayyana bayanin da aka yi mana na hujjojin da muke da su ba, kuma mun yi amannar cewa ba mu aikata ba daidai ba kuma muna da hujja.
"Sai dai duk da haka mun yanke shawarar cewa ba za mu daukaka kara ba," in ji Shugaban Juventus Gianluca Ferrero.
Ferrero ya ce matakin Juventus na kin daukaka kara ya dace da manufar sulhu da Hukumar Kwallon Kafar Italiya (FIGC) a watan Mayu, inda kungiyar ta amince ta biya tarar Yuro 718,000 sannan ta yarda ba za ta kalubalanci matakin cire mata maki 10 ba da aka yi.
"Kamar yadda ya faru a wancan batun, mun yanke shawarar kawo karshen wannan yanayi na rashin tabbas kuma mun bai wa masu ruwa da tsaki a kungiyar tabbacin cewa kungiyar za ta fafata a manyan gasa zuwa gaba," in ji Ferrero.
"Daukaka a gaban kotu wanda ba a san hukuncin da za a yanke ba a karshe, za ta kara haifar da yanayi na rashin tabbas kan yiwuwar shigarmu gasar Zakarun Turai ta kakar 2024 zuwa 2025."
An fara wasannin neman gurbin shiga Conference League din ne na kakar 2023 zuwa 2024 a farkon watan nan.