Mogoya bayan ƙungiyar ƙwallon kafa ta China suna murya a wani wasa da aka kara da Indiya inda aka tashi babu ci/ Hoto: AFP

Wata kotu a China a ranar Litinin ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru 11 ga tsohon mataimakin shugaban hukumar ƙwallon kafa ta ƙasar (CFA), bisa kama shi da laifin karɓar cin hanci da rashawa a harkokin wasanni.

Kotun Jingzhou da ke lardin Hubei ce ta yanke wa Li Yuyi hukuncin zaman gidan yari.

Kazalika kotun ta yanke wa Li biyan tarar dala 140,000, tare da ba da umarnin a ƙwace kadarorin da ya samu ta hanyar cin hanci da rashawa kana a miƙa su ga gwamnatin ta China, in ji kotun.

A watan Maris, Li ya amsa laifinsa na yin amfani da mukaminsa a CFA wajen tara kudi da kyaututtuka da suka kai har dala miliyan 1.7 tsakanin shekarar 2004 zuwa 2021, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na faransa AFP ya rawaito.

Li ya riƙe mukamin mataimakin shugaban hukumar CFA daga shekarar 2015 zuwa 2019, kafin lokacin da ya kasance shugaban kula da harkokin wasanni na Shanghai.

Hukumomi sun duƙufa wajen ɗaukar tsauraran matakai na daƙile ayyukan cin hanci da rashawa a fannin wasanni a China karkashin mulkin Shugaba Xi Jinping, musamman a fannin ƙwallon ƙafa.

Shugaban Xi dai ya taɓa furta cewa, yana da burin kasarsa ta karbi baƙuncin gasar cin kofin duniya tare da lashe gasar baki ɗaya.

Sai dai, da kamar wuya cika wannan burin sakamakon yawan badaƙalar cin hanci da rashawa ake samu da kuma rashin sakamako mai kyau a filin wasa.

An yanke wa tsohon shugaban hukumar CFA Chen Xuyuan hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari a watan Maris saboda kama shi da laifin karɓar cin hancin da ya haura dala miliyan 11.

Har ilau a watan ne, tsohon kocin tawagar ƙungiyar ƙwallon kafa ta China kana tsohon ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar Everton Li Tie ya amsa laifin karbar cin hanci na sama da dala miliyan 10.7 tare da taimaka wa wajen canja jaddawalin wasanni.

Sannan a watan Mayu ne, kafar yada labarai ta CCTV a ƙasar ta fitar da wani rahoto kan cewa, Gou Zhongwen, tsohon daraktan hukumar kula da wasannin matsa jiki ta China, yana fuskantar bincike kan zargin cin hanci da rashawa.

Haka kuma, a 'yan watannin nan, kimanin manyan jami'an hukumar CFA goma ne ake gudanar da bincike a kan su kan badaƙalar cin hanci da rashawa.

AFP