Biniam Girmay shi ne baƙar fata na farko da ya taɓa lashe gasar Tour de France,/ Hoto: Getty

Ɗan wasan tseren keke na ƙasar Eritrea Biniam Girmay ya kafa tarihi a nasarar da ya samu a gasar Tour de France na mataki na 12 a bana.

Girmay ɗan asalin ƙasar Eritiriya ya zama Baƙar fata na farko da ya taɓa lashe gasar Tour de France, inda ya samu nasarar farko a mataki na uku a wasan a ranar 1 ga watan Yulin bana kana yayi nasara a mataki na takwas.

Ɗan wasan mai shekaru 24, ya doke Wout van Aert na Belgium a tseren kilomita 40 na ƙarshe a Villeneuve-sur-Lot, inda ya tabbatar da kansa a matsayin wanda ya fi gudu a gasar tseren keke na shekarar 2024.

A yanzu Girmay ya riƙe kambunsa na jagoranci a gasar green jersey da maki 111 inda ya sha gaban wanda yake biye masa, Jasper Philipsen daga Belgium.

'Ina ji na a matsayin mai gudu'

"Gasar green jersey ta ba ni fuka-fukai; ina jina ina da gudu sosai. Gudun a hannu yake. Na ɗan sha wahala a wannan kakar wasannin baya-bayan nan, amma na sauya a bana, kuma ina samun nasara," a cewar Girmay.

An gudanar da tseren The Tour de France Stage 13 ce ranar Juma'a, wacce ake tafiyar kilomita 165.5 daga Agen zuwa Pau.

TRT Afrika