Hukumar gasar Firimiya ta sanar ranar Litinin cewa, an saka mashahurin ɗan wasan ƙwallo Ashley Cole cikin Kundin Shahara na gasar Firimiya.
Ashley Cole ya ce, "An karrama ni da aka saka ni cikin Kundin Shahara na Gasar Firimiya. Abin farin ciki ne a ce an karrama ni a ƙarshen rayuwata ta ƙwallon ƙafa."
An faɗa a shafin X cewa, "Ashley Cole babban mai tsaron baya ne wanda ake girmamawa saboda gwanintarsa. Kuma shi ne na farko da aka karrama a shekarar 2024".
Sanarwar da aka wallafa a shafin intanet na gasar ta ce, "Ashley Cole ya kasance mai hanzari da naci da juriya, yayin da ya samar da salon wasan baya a fagen ƙwallon ƙafa na Ingila".
"Matashin ɗan wasan da ya zamo dattijo a ɓangaren baya daga hagu, ya kasance mara tsoro wajen tare ƙwallo, ga gwarzantaka wajen kai hari, kuma hazaƙarsa ta kai shi matsayin shahara a tarihin gasar."
'Ina alfahari'
Ashley Cole ya ce, "Ina shauƙin tuna baya ganin yadda muka yi aiki tuƙuru. Samun shiga Kundin Shahara tare da manyan 'yan wasa irinsu Alan Shearer, da Thiery Henry, da Didier Drogba da Rio Ferdinand, ya sa ina alfahari da wannan kundi."
Cole ya yi ritaya daga ƙwallo a 2019 yana da shekaru 38, inda ya yi shekaru 20 yana buga ƙwallo.
Yanzu yana da shekaru 43, kuma ya buga wasannin gasar Firimiya har sau 385, inda ya ci ƙwallaye 15 tare da bayar da tallafin cin 31.
Taka rawa a Chelsea
Ashley Cole ya shafe yawancin shekarunsa na wasa a ƙungiyar Chelsea, inda ya buga wasa daga 2006 zuwa 2014.
Haka nan kuma, ya yi wasa a Arsenal, da Crystal Palace, da Derby County, da Los Angeles Galaxy a Amurka, da kuma a Italiya inda ya buga wa AS Roma.
Ɗan wasan wanda ɗan asalin Ingila ne, ya lashe kofin Zakarun Turai na UEFA, da kuma kofin gasar Europa League, duka a lokacin da yake buga wa Chelsea.
Sannan ya ci kofin gasar Firimiya har sau biyu tare da Arsenal, sai guda ɗaya tare da Chelsea.