Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce dole ne kungiyar ta karfafa kanta ta hanyar sayen 'yan wasa a kasuwar musayar 'yan kwallo idan tana so ta kayar da Manchester City a gasar Firimiya a kaka mai zuwa.
Arsenal ce ta fi zama a kan gaba a galibin kakar wasan da ta wuce, amma ta fuskanci tasgaro bayan manyan 'yan wasanta sun yi fama da raunuka.
City ta lashe kofinta na hudu a Gasar Firimiya a shekaru biyar sannan ta dauki kofuna uku a kakar wasan da ta wuce: kufunan gasar firimiya, FA da kuma Zakarun Turai.
Rahotanni sun ce kungiyoyin biyu suna neman daukar kyaftin din West Ham captain Declan Rice, yayin da kuma ake sa rai Arsenal za ta dauki Kai Havertz daga Chelsea.
"Wannan shi ne burinmu," in ji Arteta a tattaunawarsa da Marca game da fatansa na lashe gasar firimiya.
"Mun san wahalar yin haka: kofun shi ne mafi shahara a duniya kuma kakar wasa mai zuwa za ta kasance mai zafi a tarihin gasar firimiya.
"Kun san abin da ya sa? Saboda abin da ya faru bara. Na kwashe shekara 22 ina wannan harkar kuma ban taba ganin gasa mai zafi irin wannan karon ba. Akwai inganci da tsare-tsare da kudi da kuma koci-koci kwararru.
Mutane kadan ne suke tunanin Arsenalza ta taka rawa a kaka mai zuwa ganin cewa ba ta cikin hudun farko a kakar wasa shida da suka wuce.
Arteta ya ce har yanzu yana jin haushin rashin daukar kofin firimiya ganin cewa yana kan gaba a gasar daga watan Agusta zuwa Afrilu.
"Har yau din nan, ina jin haushi kasancewa ban lashe Gasar Firimiya ba bayan na yi wata 10 ina fafatawa da City," in ji shi.