Tsohon dan wasan Chelsea da Arsenal Cesc Fabregas ya yi ritaya daga kwallon kafa

Tsohon dan wasan Chelsea da Arsenal Cesc Fabregas ya yi ritaya daga kwallon kafa

"Ina cike da bakin cikin sanar da ku cewa lokaci ya yi da zan ajiye takalman wasan kwallon kafana," in ji Fabregas.
Fabregas ya taimaka wa Sifaniya wurin lashe Kofin Duniya, ya dauki kofin Gasar Firimiya sau biyu a Chelsea da kuma La Liga sau daya a Barcelona./Hoto: Getty

Tsohon dan wasan tsakiyar Arsenal, Barcelona da Chelsea Cesc Fabregas ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafa.

Dan wasan mai shekara 36 ya sanar da yin ritayarsa ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Asabar.

"Ina cike da bakin cikin sanar da ku cewa lokaci ya yi da zan ajiye takalman wasan kwallon kafana," in ji Fabregas.

Ya yi ritaya ne shekara daya bayan ya sanya hannu a kwantaragin shekara biyu da kungiyar kwallon kafar Como da ke fafata gasar Serie B a Italiya.

"Ba bakin ciki ne kawai ba, domin kuwa zan soma aikin horar da 'yan wasan kwallon kafa a rukunin B da Primavera na Como 1907," a cewarsa.

Fabregas ya taimaka wa Sifaniya wurin lashe Kofin Duniya, ya dauki kofin Gasar Firimiya sau biyu a Chelsea da kuma La Liga sau daya a Barcelona.

TRT Afrika