Idan dai ba wata matsala aka samu ba, ana ganin Harry Kane zai koma Bayern Munich da taka leda nan da mako mai zuwa:Hoto/Reuters

Dan wasan gaban Ingila, Harry Kane ya shirya domin ya je a gwada lafiyarsa a Bayern Munich bayan kungiyarsa ta Tottenham ta ba shi izinin tafiya Jamus.

Tun ranar Alhamis ne dai kungiyoyin Bayern da Spurs suka cimma yarjejeniyar cinikin kudi sama da fam miliyan 86.4 a kan dan wasan mai shekara 30.

Akwai alamar cewa Kane, wanda shi ne dan kwallon da ya fi zura wa Spurs kwallo a raga a tarihi inda ya zura kwallaye 280 a raga, ya yanke shawarar komawa kungiyar ta Bundesliga.

Kwantiragin Kane da kungiyarsa ta Gasar Firimiyar Ingila din dai saura shekara daya kafin kungiyar ta tsayar da magana da Bayern Munich ta Jamus.

Ana sa ran dan wasan zai karasa komawa a Jamus da taka leda a cikin mako mai zuwa idan dai ba a samu wata matsala ba.

A da dai an alakanta dan wasan da komawa Manchester United, sai dai babu tabbacin ko shugaban Spurs zai so ya sayar da dan wasan ga wani kulob din gasar Firimiya.

Ko a shekarar 2021 ma Manchester City ta nemi ta sayi Kane, lamarin da ya sa dan wasan ya jinkirta komawarsa sansanin horarwar Tottenham din gabannin fara kakar 2021.

TRT Afrika