Chelsea ta cimma yarjejeniyar sayar da Hakim Ziyech ga kungiyar Galatasaray ta kasar Turkiyya.
A halin yanzu dai ana sa ran dan wasan na Morocco, Hakim Ziyech, zai je a gwada lafiyarsa a kungiyar ta gasar Super Lig da ke birnin Santambul.
Dan wasan, mai shekara 30, ba ya cikin wadanda ake damawa da su a Stamford Bridge kuma a baya ya yi kokarin tafiya Paris St-Germain da Al Nassr da ke Saudiyya.
Ziyech ya buga wa Chelsea wasa 107 a dukkan gasanni tun lokacin da ya koma kungiyar a shekarar 2020 kan kudi fam miliyan 33.3.
Tsohon dan wasan na Ajax ya zauna a benci ne yayin da Blues suka yi nasarar lashe kofin zakarun Turai a shekarar 2021 kuma daya ne daga cikin manyan ‘yan wasa Morocco da suka kafa tarihi na kasancewa tawagar Afirka ta farko da kai matakin dab da na karshe a gasar cin Kofin Duniya da aka yi a Qatar a 2022.
Sai dai kuma ya koma cikin sauran ‘yan wasan da ba su da muhimmacin a kungiyar tun lokacin da kungiyar ta kashe kimamin fam miliyan 900 kan ‘yan wasa.
Ziyech ba ya cikin ‘yan wasan Chelsea da suka yi atisayen gabanin kakar bana a Amurka ba kuma ba ya cikin ‘yan wasan kungiyar da suka taka leda a karawar kungiyar da Liverpool inda suka yi canjaras a farkon wannan kakar.