Wannan ne karo na farko da kungiyar kwallon kafa ta Nijar ta 'yan kasa da shekara 23 ta samu wannan gurbi Photo/ AA

Shugaban Jamhuriyyar Nijar Mohamed Bazoum ya taya tawagar kwallon kafa ta kasar murnar samun gurbi domin buga gasar kwallon kafa ta Afirka ta ‘yan kasa da shekara 23.

Bazoum ya taya murnar ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce jajircewa da sadaukar da kai da matasan ‘yan wasan suka yi da masu horas da su ne ya kai su ga nasara.

“Nijar na alfahari da ku,” in ji Shugaba Bazoum.

Kungiyar kwallon kafa ta Nijar dai ta kara ne da Sudan inda Nijar din ta lallasa Sudan da ci 2-1.

Kasar Moroko ce dai za ta karbi bakuncin wannan gasa ta gasar kwallon Afirka ta ‘yan kasa da shekara 23 wato AFCON U-23.

Kasashen da suka samu gurbin buga gasar sun hada da Masar da Congo da Ghana da Gabon da Guinea.

Sauran sun hada da Mali da Nijar da mai masaukin baki wato Moroko wadda ita kai tsaye ta samu gurbi sakamakon ita ce mai masaukin baki.

Kasashen da suka yi nasarar zuwa na daya da na biyu da na uku za su samu gurbin zuwa gasar kwallon kafa ta Olympics ta bazara wadda za a yi a Paris.

TRT Afrika da abokan hulda