Moses Simon ne ya zura wa Nijeriya kwallo a ragar Guinea-Bissau

Tawagar kwallon kafa ta Nijeriya ta dau fansa kan tawagar kwallon kafar Guinea-Bissau yayin da ta doke Guinea-Bissau da ci daya da nema a filin wasan Estádio Nacional 24 da ke Bissau, a cigaba da wasannin neman shiga Gasar Cin Kofin Afirka (AFCON 2023).

A wasan da aka yi ranar Litinin, Moses Simon ne ya zura wa Nijeriya kwallon da bugun fanareti minti 30 da fara wasa, kuma aka gama wasan a haka kamar yadda Guinea-Bissau ta doke Nijeriya a Abuja a ranar Juma’a.

Kazalika cikin wasannin da aka yi ranar Litinin din Kongo ta doke Sudan Ta Kudu da ci daya mai ban haushi, yayin da Angola da Ghana suka yi canjaras.

Aljeriya ta doke Nijar a gidanta da ci daya da nema, yayin ita kuma Guinea-Konakry ta doke Habasha a gidanta da 3-2.

Kasar Sudan ta doke Gabon da ci daya mai ban haushi.

Wasannin Talata

Cikin wasannin da za a yi ranar Talata na neman shigan Gasar ta Cin Kofin Afirka (AFCON 2023), akwai karawar Malawi da Masar da karfe biyu agogon Nijeriya da karawar Namibiya da Kamaru, shi ma da karfe biyu agogon Nijeriya din.

Eswatini za ta kara da Cape Verde yayin da Bostwana za ta hadu da Equitorial Guinea duka da karfe biyu agogon Nijeriya.

Da karfe biyar agogon Nijeriya kuma, Laberiya za ta hadu da Afirka ta Kudu yayin da ita kuma Namibiya za ta hadu da Kamaru.

Har ila yau, Muzambik za ta karbi bakuncin kasar Senegal da karfe biyar agogon Nijeriya.

Kasar Senegal wadda take rike da kofin tana cikin kasashen dake yakin neman shiga gasar ta cin kofin Afirka/Photo AP

Idan aka leka Tanzaniya kuma tawagar kwallon kafar kasar ce za ta kara da takwararta ta Uganda da karfe shida agogon Nijeriya, yayin da ita kuwa Komoros za ta karbi bakuncin Ivory Coast da karfe takwas agogon Nijeriya.

Togo za ta kara da Burkina Faso yayin da Libiya za ta kara da Tunisiya duka a karfe takwas agogon Nijeriya.

Da karfe 11 na daren Talata agogon Nijeriya kuma kasar Mauritaniya ce za ta kara da kasar Jamhuriyar Dimokradiyar Kongo.

Kasashe 24 ne dai za su samu damar shiga gasar wadda za a yi a kasar Ivory Coast.